Home Back

Wani Dansanda Mai Rakiyar Jirgin Kasan Kaduna Zuwa Abuja Ya Rasu Acikin Jirgin

leadership.ng 2024/5/19
Wani Dansanda Mai Rakiyar Jirgin Kasan Kaduna Zuwa Abuja Ya Rasu Acikin Jirgin

Daya daga cikin ‘yansandan da ke rakiyar jirgin kasan da ya taso daga Kaduna zuwa Abuja ya rasa ransa yayin da yake rakiyar jirgin a ranar Alhamis.

An ce, dansandan yana cikin koshin lafiya yayin da jirgin ya taso daga tashar jirgin da ke Rigasa.

Wani ganau ya shaida cewa, marigayin ya koka da ciwon kirji kafin ya rasu.

Jirgin ya isa Kubwa a Abuja da misalin karfe 3:20 inda fasinjoji suka sauka.

Har zuwa lokacin da aka hada wannan rahoto, LEADERSHIP ta kasa jin ta bakin kakakin hukumar kula da jiragen kasa ta Nijeriya (NRC).

People are also reading