Home Back

Shekara Ɗaya Ta Mulkin Tinubu: Nijeriya Ta Fara Ganin Sauyi Wajen Samun Kwanciyar Hankali Da Arziki Da Tsaro – Minista

leadership.ng 2024/6/26
Shekara Ɗaya Ta Mulkin Tinubu: Nijeriya Ta Fara Ganin Sauyi Wajen Samun Kwanciyar Hankali Da Arziki Da Tsaro – Minista

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce Nijeriya ta fara tafiya mai kawo sauyi ta fuskar samun kwanciyar hankali da arziki da tsaro, wanda Ajandar Sabunta Fata Mai Lamba 8 ta ƙunsa a cikin shekara ta farko tun bayan hawan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Ministan ya bayyana haka ne a cikin wani rahoto da ma’aikatar sa ta fitar a ranar Talata mai taken “Shekara Ɗaya ta Gwamnatin Tinubu – Gina Nijeriya mai Tsaro, Ƙarfi, da Wadata,” wanda ke bayyana gagarumin cigaban da aka samu a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu, na tunkarar manyan matsalolin ƙasa da aiwatar da ingantattun manufofi da nufin samar da haɓaka da cigaban ƙasa.

Rahoton ya ce, “A yayin da ake fama da matsalolin tattalin arziki da tashe-tashen hankula da rashin aikin yi suka haifar, sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnati ta yi sun daidaita tattalin arzikin ƙasar tare da haifar da cigaba.

“Wani muhimmin yunƙuri shi ne kawar da tallafin man fetur maras ɗorewa, da karkatar da kusan dala biliyan 10 kowace shekara zuwa sassa masu muhimmanci kamar kiwon lafiya, ilimi, ababen more rayuwa, da tsaro.

“Wannan mataki kaɗai ya haifar da raguwar shigo da mai da kashi 50 cikin 100 tare da ƙaruwar kuɗaɗen shiga na jihohi da ƙananan hukumomi. Kawar da tallafin kuɗin ƙasashen waje da kuma daidaita farashin canji ya ƙarfafa tattalin arzikin Nijeriya, wanda hakan ya sanya Kasuwar Hada-hadar Hannun Jari ta Nijeriya ta zama kan gaba a kasuwannin duniya tare da ƙarfafa darajar Naira.”

Rahoton ya ƙara da cewa, “Domin samun sauƙin tasirin waɗannan matakan tattalin arziki, gwamnatin ta ƙaddamar da wasu ayyuka da suka haɗa da biyan albashin naira 35,000 ga ma’aikatan gwamnati duk wata, kafa kwamitin sake fasalin albashi, da kuma samar da Asusun Tallafa wa Jihohi.

“Ɓangaren ƙasa da ƙasa, gwamnatin ta samu nasarar jawo jarin sama da dala biliyan 30, wanda hakan ya ƙara haɓaka tattalin arzikin Nijeriya.

“Tsaro ya kasance babban abin da aka fi mayar da hankali a kan shi, tare da zuba jari mai yawa da nufin zamanintar da rundunonin sojoji da kuma cimma muhimman nasarori a harkar tsaron ƙasa.

“Wannan yunƙurin ya haifar da ‘yantar da mutane sama da 4,600 da aka yi garkuwa da su, tare da kawar da masu laifi 9,300, tare da kama ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga 7,000.

“Jami’an tsaron sun kuma ƙwato dubban makamai da harsasai, wanda hakan na da muhimmanci wajen yaƙar ‘yan fashi da masu tayar da ƙayar baya.

A yayin da yake tunkarar matsalar samar da abinci, Shugaba Tinubu ya kafa dokar ta-ɓaci, wanda ya kai ga sake fasalin Ma’aikatar Noma zuwa Ma’aikatar Noma da Samar da Abinci.

An ƙaddamar da shirye-shirye irin su Asusun Bunƙasa Noma na Ƙasa da Shirin Noman Rani don bunƙasa aikin noma da tabbatar da wadatar abinci.

“An inganta matakan tsaro wajen kula da makamashi da albarkatun ƙasa a yankin Neja Delta, lamarin da ya haifar da ƙaruwar haƙo mai da ƙarin iskar gas. Haka kuma an ba da fifiko wajen samar da ababen more rayuwa, tare da zuba jari mai yawa a hanyoyin sufuri da suka haɗa da ƙaddamar da sabbin layukan dogo da ƙaddamar da babban titin Legas zuwa Kalaba, da ƙaddamar da Tsarin Babbar Hanyar Sokoto zuwa Badagry.

“An haɓaka fannin kiwon lafiya da ilimi sosai a ƙarƙashin Ajandar Sabunta Fata. Faɗaɗa cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko da gabatar da dokar ba da lamuni ga ɗalibai (Samun Ilimi Mai Girma) wani ɓangare ne na ƙoƙarin inganta hanyoyin samun muhimman ayyuka da damarmaki ga dukkan ‘yan Nijeriya.

“A yayin da muke ci gaba da tafiya, gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da jajircewa wajen ganin ta na tabbatar da Nijeriya mai ɗorewa da wadatar arziki, wadda za ta kasance ƙarƙashin zuba jari, da ƙarfafa matasa, da inganta harkokin mulki.

“Cigaban da aka samu a cikin shekara guda kacal ya kafa ginshiƙin haɓaka da cigaba mai ɗorewa, tare da yin alƙawarin samun kyakkyawar rayuwa a nan gaba ga dukkan ‘yan Nijeriya.”

People are also reading