Home Back

Mun kama wasu maniyyata da yunƙurin safarar miyagun ƙwayoyi zuwa Saudiyya – NDLEA

dalafmkano.com 2024/7/3

Hukumar hana sha da safarar miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta kama wasu maniyyata aikin hajjin bana su huɗu, bisa zargin su da yunƙurin safarar miyagun ƙwayoyi zuwa kasa mai tsarki.

Kwamnadan hukumar NDLEA, na jihar Legas Abubakar Liman Wali, ne ya bayyana hakan a zantawar sa da wakilimu Abba Isah Muhammad, yana mai cewa sun kama mutanen ne a lokacin da suke yunƙurin haɗiye hodar iblis ɗauri Ɗari biyu, a wani Hotal da ke yankin Oshodi a jihar ta Legas a ranar Laraba.

Mutanen dai da aka kama sun haɗar da Usman Kamorudden ɗan shekara 31, da Olasunkanmi Owolabi mai shekaru 46, da kuma Fatai Yekini ɗan shekaru 38, sai wata mace mai suna Ayinla Kemi mai shekaru 34, wanda aka kama su a wani Hotel, dai-dai lokacin da suke yunƙuri haɗiye hodar Iblis ɗin, mai kimar kilogram 2.20.

Hukumar ta kuma ce jami’an su za su ci gaba da aiki, tare da magance matsalar miyagun kwayoyi yayin a maniyyatan aikin Hajjin ke ci gaba da tashi zuwa ƙasa mai tsarki.

People are also reading