Home Back

ASUU Ta Bada Wa’adin Mako 3 Ga Gwamnatin Tarayya, Ta Yi Barazanar Shiga Sabon Yajin aiki

leadership.ng 2024/6/29
ASUU Ta Bada Wa’adin Mako 3 Ga Gwamnatin Tarayya, Ta Yi Barazanar Shiga Sabon Yajin aiki

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta bayar da wa’adin makonni uku ga Gwamnatin Tarayya, inda ta bukaci a warware matsalolin da suka daɗe suna fama da su domin kaucewa yajin aikin da ake shirin shiga.

Shugaban ƙungiyar ASUU reshen Jami’ar Dutse (FUD) jihar Jigawa, Kwamared Salim Ahmed ne ya bayyana hakan a lokacin wani taron manema labarai na gaggawa.

Ahmed ya soki gwamnatin shugaba ƙasa Bola Tinubu, saboda yin watsi da yunƙurin ƙungiyar na shiga tattaunawa. Batutuwan da ba a warware ba sun haɗa da sake tattaunawa kan yarjejeniyar FGN/ASUU na 2009, jin dadin mambobin ƙungiyar, da cin gashin kan jami’o’i, da samar da kuɗaɗe, da kuma rusa majalisar gudanarwa ba tare da izini ba.

Ƙungiyar ASUU ta kuma bayyana rashin aiki da tsarin Integrated Payroll and Personnel Information System (IPPIS) da kuma rashin biyan kuɗaɗen alawus na Ilimi (EAA).

Ƙungiyar malaman jami’o’i ta ASUU ta shirya zaburar da mambobinta da wayar da kan al’umma cikin makonni uku masu zuwa. Ahmed ya buƙaci masu ruwa da tsaki da su matsa wa gwamnati lamba domin ta gana da ƙungiyar domin hana afkuwar rikicin da za a iya kaucewa a cikin tsarin jami’o’in.

Ƙungiyar ta jaddada cewa, rashin magance waɗannan matsalolin na iya haifar da ɗaukar matakai na yakin aiki, tare da ƙara kawo cikas ga ɓangaren ilimi da ke da rauni na Nijeriya.

People are also reading