Home Back

Faransa ta kama hanyar shiga sabon babin siyasa na daban

bbc.com 2024/8/24
Masu zabe a Faransa na murna

Asalin hoton, OTHERS

Hadakar masu ra’ayin kawo sauyi ta samu nasarar kawar da baranazar jam'iyyar masu tsattsauran ra’ayin rikau ta National Rally a zaben ‘yan majalisar dokoki da aka yi ranar Lahadi a Faransa, inda hadakar ta samu kujeru mafiya yawa, yayin da ta masu ra’ayin mazan jiyan ta kasance ta uku.

Sai dai sakamakon ya kasance yanzu babu wani bangare cikin bangarori uku na siyasar kasar da ke da yawan kujerun da yake da rinajyen kafa gwamnati.

Zaben zagayen farko da aka yi na makon da ya gabata wanda ya ba wa masu ra’ayin rikau din nasara ya sa an yi ta hasashen a wannan karon ma za su yi nasara, to amma lamarin ya sha bamban.

Sabuwar hadakar masu ra’ayin kawo sauyi, New Popular Front, ta taka rawar gani a zaben da aka yi na majalisar dokoki zagaye na biyu ranar Lahadi da ya ba ta kujeru mafiya yawa ya sa ta zama ta daya.

Yayin da jam'iyyar Shugaba Macron ta hadakar masu matsakaicin ra’ayi ta jo ta biyu, sai kuma jamiyyar masu tsattsauranarin rikau ta National rally wadda amakon da ya gabata ta bayar da mamaki inda ta sha gaban sauran, lamarin da ya sa hatta masu hasashe suka tsinkayi cewa za ta maimaita a wannan karon ma.

Sai dai ina fitar dango da magoya bayan sauran bangarorin biyu wadanda kusan ta su ta fi jtuwa a kan tafiya ta masu ra’ayin mazan jiyan ta sa suka mayar da National Rally din kurar baya, ta uku.

Hakan ya kasance ne bayan da wasu ‘yan takarar wadancan bangarorin biyu suka yi wa masu ra’ayin rikau taron kusan dangi inda siuka rika janye wa juna, domin kuri’unsu su karkata waje daya, inda wannan dabara ta kai musu a yanzu.

Ana sa ran idan aka fitar da dukkanin alkaluma sabuwar hadakar masu ra’ayin kawo sauyin ta New Popular Front ta sami kujeru 182 daga cikin kujerun majalisar kasar ta Faransa 577, yayin da hadakar su Shugaba Macron ta samu kujeru 168, sai kuma National Rally da ta zame musu barazana ta tayar da su hadakar da ba shirin za ta samu kujeru 60.

Wanda hakan zai sa a samu majalisar dokokin da ba jamiyyar da ke da gagarumin rinjayen da ya kamata ta tsaya da kafarta ta kafa gwamnati – tuwona maina

Zuwa yanzu dai Shugaba Macron wanda ake ganin ya kira wannan ruwa sakamakon zabe na wuri da ya kira bayan da d masu tsatsauran ra’ayin rikau din suka yi nasara a zaben majalisar dokokin Turai bai nuna alamar abin da zai yi ba, kafin ya tashi zuwa Washoington domin halartar tsaron kolin kungiyar tsaro ta NATO a wannan makon.

To amma Firaministansa, Gabriel Attal, ya ce zai sauka kodayake yana da niuyyar ci gaba da zama har zuwa kammala gasar wasannin Olympics da za a yi a watan nan na Yuli birnin Paris.

Wannan ya sa yanzu ba a san waye zai kasance firaminista na gaba ba.

People are also reading