Home Back

Mace Za Ta Iya Yin I’itikafi A Wannan Zamanin?

leadership.ng 2024/5/15
Ramadan

Assalamu Alaikum, malam mene ne hukuncin ittikafin mata a musulunci musamman a wannan zamanin?

Wa alaikum asssalam, ya halatta mace ta yi i’itikafi, saboda matayen Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sun yi i’itikafi kamar yadda ya zo a sahihil Bukhari. Yana daga cikin ka’idoji a usulul fikhi duk hukuncin da ya zo a shari’a yana hade mata da maza, sai idan an samu dalilin da ya kebance maza kawai. I’itikafi ibada ce tabbatacciya a musulunci wacce Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya aikata ta saboda neman kusanci da Allah a watan Ramdhana, babu bambanci tsakanin mace da namiji wajan koyi da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a wannan ibadar, sai dai kar matar aure ta fita sai ta nemi iznin mijinta.
Allah ne mafi sani.

People are also reading