Home Back

Kano: Takaddama Yayin da Tsagin APC Ya Sake Dakatar da Ganduje Kan Wasu Sabbin Dalillai

legit.ng 2024/5/19

Wani tsagin jam'iyyar APC a gundumar Ganduje ya sake tabbatar da korar Abdullahi Ganduje daga jam'iyyar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Sabuwar takaddama yayin da tsagin jam'iyyar APC a matakin unguwa ya sake dakatar da Abdullahi Ganduje a jami'yyar.

Jam'iyyar ta dauki matakin ne bayan wani tsagin jam'iyyar a Ganduje da ke karamar hukumar Dawakin Tofa ya musanta dakatar da Ganduje.

Yayin da ya ke zantawa da manema labarai, sakataren jam'iyyar a Unguwar Ganduje, Ja'afar Adamu Ganduje ya ce sun dauki matakin ne a madadin masu ruwa da tsakin jam'iyyar 11.

Ja'afar ya ce sun dakatar da tsohon gwamnan ne kan zargin cin dunduniyar jami'yyar da ya jawo mata rashin nasara a zaben 2023.

Ya ce cin amanar jami'yyar da ya yi ya jawo rashin nasara musamman a zaben jihar Kano da aka gudanar, cewar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adamu wanda ɗan uwa ne ga Ganduje ya ce ayyukan tsohon gwamnan ya kawo rikici a jami'yyar da ke neman wargaza ta.

Ya kuma zargi Ganduje da rashin biyan kudin jam'iyyar wanda hakan ya sabawa dokar jami'yyar.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

People are also reading