Home Back

Xi Jinping: Sin Za Ta Ci Gaba Da Kasancewa Cikin Rukunin Kasashe Masu Tasowa

leadership.ng 2024/6/26
Xi Jinping: Sin Za Ta Ci Gaba Da Kasancewa Cikin Rukunin Kasashe Masu Tasowa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce kasarsa ta kasance, kuma za ta ci gaba da kasancewa cikin rukunin kasashe masu tasowa a ko da yaushe.

Xi Jinping ya bayyana haka ne cikin jawabin da ya gabatar ta kafar bidiyo, yayin bude bikin murnar cika shekaru 60 da kafuwar Dandalin Tattauna Harkokin Cinikayya da Ci Gaba na MDD (UNCTAD).

Shugaban na kasar Sin ya nanata bukatar hada hannu wajen gina al’umma mai makoma ta bai daya ga dukkan bil Adama ta hanya mai dacewa da tarihi da muradun jama’a, yayin da duniya ke fuskantar sauye-sauye cikin sauri da sabbin kalubale a bangaren zaman lafiya da ci gaba.

Ya kuma bukaci kasashe, musamman manya, da su aiwatar da hadin gwiwar da ta kunshi bangarori daban daban da mara baya ga samar da tsarin duniya mai daidaito tsakanin kasashe, da kiyaye manufofi da ka’idojin MDD da kuma taimakawa dandalin UNCTAD da sauran cibiyoyin kasa da kasa, wajen kyautata rawar da suke takawa.

Ya ce, a bana ake cika shekaru 75 da kafuwar Kamhuriyar Jama’ar Kasar Sin, kuma kasar Sin na samun ci gaba wajen zamanantar da kanta ta kowacce fuska ta hanyar samun ci gaba mai inganci, wanda zai samar da karin damarmaki ga ci gaban duniya. Ya ce, har kullum, kasar Sin za ta ci gaba da kasancewa mambar rukunin kasashe masu tasowa.

Bugu da kari, ya ce, Sin za ta fadada shigo da kayayyaki daga sauran kasashe masu tasowa da karfafa cinikayya da zuba jari da hadin gwiwar neman ci gaba tare da su, da kuma kara azama kan aiwatar da ajandar MDD ta samun ci gaba mai dorewa ta nan da shekarar 2030. (Fa’iza Mustapha)

People are also reading