Home Back

' Bata -gari na kokarin tayar da husuma a wasu muhiman wurare da ke Kano'

bbc.com 2024/7/3

Asalin hoton, Getty Images

Kano
Bayanan hoto, Rundunar 'yan sandan jihar Kano

Kwamishinan rundunar ‘yan sanda jihar Kano, Mohammed Hussein Gumel ya ce jami'an tsaro sun sami bayannan sirri masu karfi wadanda suka yi zargin cewa bata-gari na kokarin tayar da tarzoma a birnin kanon ta hanyar kai hare -hare a wasu muhiman wurare ciki har da Majalisar dokokin Jihar.

Mohammed Hussein Gumel ya shaida wa manema labarai cewa tuni suka dauki matakan dakile yunkurin:

''Ina son na sanar da ku cewa mun kamala shirye-shiryen inganta sintirin tsaro tare da tsaurara matakan tsaro a wuraren da ake son a kai wa hari tare da zuba ido maboyarsu'', in ji shi.

Game da umarnin da kotu ta bayar inda ta nemi a dakatar da matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka na rushe masarautu biyar, CP Gumel ya dage da cewa dukannin hukukomin tsaron jihar suna mutuntunta umarnin kotu:

''Duk wani abu da ya dabaibaye al’amuran masarautu muna kallonsa a matsayin wani bangare na doka da kuma bangaren umarnin kotu''

''A matsayinmu na hukumar da ke tilasta bin doka da oda idan kotu ta bada umarni, ko da daidai ne ko akasin haka, to zamu bi shi sau da kafa har zuwa lokacin da kotun ta yanke hukuncin kan al'amarin'' in ji shi.

Ita ma rundunar sojin Najeriya ta ce ba bu hannunta a rikicin masarautar Kano kuma ba bu ruwanta wajan aiwatar da umarnin kotu.

A cikin sanarwa da ke dauke da sa hannun daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin kasar, Manjo Janarar Onyema Nwachukwu ya ce sun dauki ‘matakin dakile masu kokarin tayar da zaune tsaye ne ’

Sojojin Najeriya na maida martani ne kan zargin da kungiyar lauyoyi ta kasa reshen jihar Kano ta yi a kan cewa sojojin na da hannu a rikicin masarautar Kano .

Bayyanai sun ce hakimai 40 ne suka hallarci zaman fadacin da Sarkin Kano Muhammad Sanusi na biyu ya yi a ranar Lahadi kuma a ciki akwai tsoffafin hakiman masarautun da aka rushe.

Sai dai masu ruwa da tsaki a masauratar Karaye da ita ma aka rushe sun yi watsi da matakin da Majalisar dokokin Jihar ta dauka.

Sun yi zargin cewa Majalisar dokokin Jihar ta dauki wannan mataki ne ba tare da tuntubar mazauna yankin ba.

People are also reading