Home Back

MDD ta yi gargadi kan halin da ake ciki a Sahel

dw.com 2024/6/28
Hoto: Fathi Nasri/AFP/Getty Images

Hukumar kula da al'amuran jinkai na MDD UNHCR, ta ce halin matsaloli musamman na tsaro da ake ciki a kasashen Nijar da Mali da ma Burkina Faso na gab da shiga kasashen da ke makwabtaka da su a halin yanzu.

Kasashe na gabar kogin Guinea da Togo da Benin da Ghana da Cote d'Ivoire dukkanin su na fama da fama da wahalhalu masu nasaba da halin tabrbarewar tsaro da na jinkai da ake ciki a kasashen na Sahel.

Abin bai ma bar kasashe irin su Mauritaniya gami da Aljeriya ba, a cewar Majalisar ta dinkin duniya.

Akalla mutum miliyan 10 da dubu 500 ne, fitintinu suka raba da sukuni a kasashen Afirka da ke fama da rikice-rikice.

People are also reading