Home Back

"Na Koyi Darasi": Obasanjo Ya Fadi Yadda Ya Ƙi Amincewa da Taimakon Tsohon Sarki a Gidan Kaso

legit.ng 2024/7/5
  • Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya tuna alherin da marigayi Lamidon Adamawa ya yi masa a gidan yari
  • Obasanjo ya bayyana yadda rayuwar gidan yari ta zama alheri a gare shi wurin ba shi damar inganta Najeriya bayan zama shugaban ƙasa
  • Wannan na zuwa ne bayan Obasanjo ya je birnin Yola na jihar Adamawa domin ƙaddamar da aiki a jiya Litinin 3 ga watan Yuni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Adamawa - Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya magantu kan halin da ya shiga a gidan yari da ke Yola.

Obasanjo ya ce zamansa a gidan kaso ya sauya masa rayuwa tare da tasiri wurin inganta Najeriya bayan ya dawo shugaban kasa.

Obasanjo ya magantu kan yadda tsohon Sarki ya taimake shi a gidan kaso
Olusegun Obasanjo ya bayyana yadda zaman gidan yari ya taimake shi inganta Najeriya. Hoto: Getty Images. Asali: Getty Images

Obasanjo ya fadi alherin zaman gidan yari

Tsohon shugaban ya bayyana haka ne a jiya Litinin 3 ga watan Yuni a Yola yayin kaddamar da wani aiki na Gwamna Ahmadu Fintiri, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce zama a gidan kaso da ke Yola ya zama masa alheri a rayuwarsa musamman bayan kasancewa shugaban kasa., ThisDay ta tattaro.

Yadda tsohon Sarki ya taimaki Obasanjo

"Lokacin da nake gidan yari a nan, marigayi Lamido ya dauke ni kamar ɗansa, ya tura min wani domin bani kyautar na'urar ba da iska (Air Condition)."
"Na ce masa Mai Martaba wanda ya saka ni a nan bai son na ji dadi, kabar ni kawai na yi fama da fanka."
"Na fada masa cewa ko da an saka hukumomi za su cire ba tare da bata lokaci ba."

- Olusegun Obasanjo

A martaninsa, Gwamna Ahmadu Fintiri ya godewa tsohon shugaban kasar kan yadda ya mutunta gayyatar da ya yi masa domin ƙaddamar da aikin.

Obasanjo ya bukaci ba matasa dama

Kun ji cewa tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya magantu kan ba matasa dama a shugabanci.

Obasanjo ya ce lokaci ya yi da ya kamata a gwada sababbin jini domin tabbatar da gudanar da shugabanci mai inganci.

Tsohon shugaban ya koka kan yadda yanzu Najeriya ta dawo ƙasa mafi hatsari da dan Adam zai yi rayuwa a ciki saboda rashin shugabanci.

Asali: Legit.ng

People are also reading