Dambarwar Sarauta: Kanawa Sun Nemi Taimakon Abba, Ƴan Daba Sun Mamaye Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Yayin da ake ci gaba da dambarwa kan sarautar Kano, mazauna birnin sun nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro.
Mazauna yankin Gwale da Dala da ke Kano sun bukaci karin jami'an ƴan sanda domin inganta tsaro.
Mutane da dama sun nuna fargaba kan yadda ake samun yawaitar ƴan daba yayin da ake rigimar sarauta a jihar, cewar Daily Nigerian.
Sun roki Gwamna Abba Kabir da ya kawo karshen matsalar baki daya wurin samar da ingantaccen tsaro.
Wani a karamar hukumar Gwale, Abubakar Mohammed ya bayyana yadda ƴan daba suka yiwa matarsa fashi a yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau, Abdulmumin Shehu da ke Dala da Aishatu Abu da ke yankin Dan Agundi sun bukaci karin jami'an tsaro a yankin.
Wannan tabarbarewar tsaro bai rasa nasaba da rigimar da ke faruwa a jihar na sarauta wanda ya kara bullar ƴan daba.
A wani labarin, kun ji cewa rundunar yan sanda ta tabbatar da dakile harin yan daba a gidan shugaban APC a Kano.
Yan daban sun yi yunkurin kutsawa gidan Abdullahi Abbas ne a ranar Juma'a 31 ga watan Mayu a karamar hukumar Gwale.
Mazauna yankin suna nuna damuwa kan yadda ƴan daba ke kara yawa musamman dalilin rigimar sarauta da ake yi a jihar.
Asali: Legit.ng