Hankula Sun Tashi Yayin da Sojan Najeriya Ya Salwantar da Ransa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Abia - Wani sojan Najeriya da ke aiki a jihar Abia ya aikata aika-aikar raba kansa da duniya.
Sojan wanda yake aiki da bataliya ta 144 Forward Operation Base (FOB) da ke High School Ngwa, Abayi, a ƙaramar hukumar Osisioma, ya salwantar da ransa.
Sojan mai suna Vitalis wanda ke da matsayin CSM, ɗan asalin Okpuala a Ngor-Okpuala a jihar Imo, ya harbe kansa a ƙofar FOB, cewar rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ba a dai san dalilin da ya sa ya yanke wannan gurguwar shawarar ba saboda babu wata sanarwa da hukumomi suka fitar, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
Wasu majiyoyi daga cikin jami’an tsaro a jihar sun bayyana cewa, bincike ne kawai zai gano ainihin abin da ya sanya ya ɗauki wannan matakin.
A cewar majiyoyi, har zuwa rasuwarsa babu wani batun yana fuskantar matsala a gidansa ko wurin aikinsa.
An tattaro cewa, sojan sai dai kawai aka neme shi aka rasa ba tare da sanin inda ya dosa ba.
Fiye da sati biyu da suka wuce ba a ji daga gare shi ba, domin abokan aikinsa da hukumomi sun kasa samunsa.
Daga nan kawai sai ya dawo sansanin sojojin sannan ya bindige kansa wanda hakan ya ba abokan aikinsa mamaki matuƙa.
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji na rundunar Operation Whirl Punch da bataliya ta musamman ta 198 ta sojojin Najeriya sun kashe ƴan ta’adda shida a jihar Kaduna.
Dakarun sojojin sun kashe ƴan ta'addan ne a wani samame da suka kai a ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar.
Asali: Legit.ng