Home Back

LAFIYA JARIN TALAKA: Bayanan Gaggawa Dangane Da Ɓarkewar Cutar Kwalara A Najeriya

premiumtimesng.com 2024/7/2
An kara wa ma’aikatan jinya na jihar Yobe albashi
HOSPITAL IN YOBE

Kwanan nan Gwamnatin Jihar Legas ta yi shelar ɓarkewar cutar kwalara a jihar, wadda cikin ‘yan kwanaki ta kashe mutum 15.

Binciken da aka gudanar a ɗakunan gwaje-gwajen cututtuka sun tabbatar da cewa cutar ta kwalara irin nau’in ‘Serovars O1 ce.

“Irin mummunar cutar kwalara ce mai saurin yaɗuwa kuma wadda ake saurin ɗauka musamman a cikin damina.” Cewar Kwamishinan Lafiya na Jihar Legas, Aikin Abayomi.

Zuwa ranar Asabar dai Kwamishina Abayomi ya tabbatar da ɓarkewar cutar wadda ya ce mutum 350 sun kamu a mazaɓu 29 da ke cikin ƙananan hukumomi daban-daban, yayin da mutum 17 ke fama da matsanancin gudawa ba tsaitsayawa.

An tabbatar da mutuwar mutum 15 tun a ranar 12 Ga Yuni, saboda tsananin gudawar da ta ƙarar da ruwan jikin su a Jihar Legas. Hakan ya nuna munin cutar sosai.

An ƙaryata raɗe-raɗi da ji-ta-ji-tar da ake ta yaɗawa a soshiyal midiya cewa wai cin gyaɗar kasshu ce ta haddasa ɓarkewar kwalarar, kuma ita ce ta kashe wasu daga cikin waɗanda kwanan na su ya ƙare.

Waɗanda ka iya kamuwa da annobar kwalara su ne mutanen da ke shan ruwa maras tsafta, masu zama cikin ƙazanta, masu fama da rashin kayan tsaftace kayan su da muhallin su, sai kuma saurin yaɗuwar da cutar ke yi ta hanyar cin abinci ko abin sha mai ɗauke da cutar.

Kwalara na haddasa gudawa da amai, ta na tsotse ruwan jiki, kuma ta na kisan gaggawa idan ba a magance ta da hanzari ba.

An yi hasashe mutum miliyan 1.3 zuwa miliyan 4 kan kamu da kwalara a kowace shekara a duniya. Kuma ta na kashe mutum daga 21,000 zuwa 143,000, kamar yadda Hukumar Daƙile Cututtuka Masu Yaɗuwa (CDC) ta bayyana.

Kwanan nan NCDC ta bayyana cewa mutum 65 sun kamu da kwalara a Najeriya, kuma cutar ta kashe mutum 30 daga 1 ga Janairu zuwa 11 ga Yuni, a ƙananan hukumomi 96 a jihohi 30.

People are also reading