Home Back

Gwamna Dauda Lawal Ya Gana Da Ministan Ruwa Domin Kammala Ayyukan Ruwa A Zamfara

leadership.ng 2024/4/29
Gwamna Dauda Lawal Ya Gana Da Ministan Ruwa Domin Kammala Ayyukan Ruwa A Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ƙara ƙaimi wajen ɗaukar nauyi tare da kammala ayyukan madatsun ruwa da ake yi a jihar.

Gwamnan ya yi kiran haka ne a ranar Talata yayin ziyarar aiki da ya kai wa Ministan Albarkatun Ruwa da Tsaftar Muhalli, Injiniya Farfesa Joseph Terlumun Utsav.

Sanarwar da mai magana da yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta ce a yayin ziyarar, an tattauna muhimman batutuwa da suka shafi ayyukan ruwa a Zamfara.

A cewarsa, Gwamna Lawal ya bayyana muhimmancin madatsun ruwa wajen samar da ruwan sha mai ɗorewa ga al’ummar jihar da kuma yadda za su bunƙasa noma da tattalin arziki baki ɗaya.

Gwamnan ya jaddada buƙatar Gwamnatin Tarayya ta ware isassun kuɗaɗe domin kammala waɗannan ayyuka, duba da irin rawar da suke takawa wajen magance matsalar ƙarancin ruwan sha a jihar da kuma bunƙasa zamantakewa da tattalin arziki.

Bugu da ƙari, Gwamna Lawal ya yi kira da a kammala tare da yin amfani da aikin madatsun ruwa a jihar domin bunƙasa noman noman rani.

A nasa jawabin, Ministan ya yi wa Gwamna Lawal alƙawarin cewa nan ba da jimawa ba za a tura tawagar ƙwararru daga ma’aikatarsa zuwa Zamfara domin tantance yanayin ruwa tare da ba da shawarar aiwatar da ayyukan da ake buƙata gaba ɗaya.

 
People are also reading