Home Back

EFCC Ta Ƙi Amincewa Da Barin Godwin Emefiele Tafiya Neman Lafiya Ƙasar Waje

leadership.ng 2024/10/6
EFCC Ta Ƙi Amincewa Da Barin Godwin Emefiele Tafiya Neman Lafiya Ƙasar Waje

Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta ƙi amincewa da buƙatar tsohon Gwamnan babban Bankin Nijeriya, Godwin Emefiele na a sake masa fasfo ɗinsa na tafiya ƙasar waje. Lauyan da ke kare Emefiele dai ya shigar da takardar shaida yana neman a ba shi fasfo din domin a ba shi damar zuwa ƙasar Ingila domin jinya, lamarin da hukumar EFCC ta yi kakkausar suka akai.

Lauyan masu gabatar da ƙara Muhammad Abbas Omeiza ya bayyana cewa babu wani rahoton likita da aka gabatar wa kotu da ke tabbatar da rashin lafiyar Emefiele da ke buƙatar jinya a ƙasashen waje.

Ya kuma ƙara da cewa, duk wata matsala ta rashin lafiya za a iya magance ta a Nijeriya, yana mai jaddada cewa Emefiele ya ajiye fasfo ɗinsa a gaban kotu a matsayin wani ɓangare na sharuɗɗan belinsa, wanda bai kamata a riƙa maganar karɓarsa ba.

Omeiza ya ƙara nuna damuwa game da yiwuwar Emefiele na iya gudawa idan ya samu jirgin sama, domin yana da alaƙa da ƙasashen duniya da zai iya haɗa baki da wasu a ƙasashen waje ya tsere.

Yayin da mai kare tsohon gwamnan Bankin ya ce wadannan duk ai na a matsayin hasashe, yana mai nuni da cewa masu gabatar da ƙara za su iya ba da sanarwar jan kunnen ƙasa da ƙasa don sauƙaƙa kama Emefiele idan ya kasa dawowa daga tafiyar da ya yi ta jinya.

Mai shari’a Mu’azu ya ɗage yanke hukunci kan ƙarar zuwa ranar 16 ga watan Yuli, 2024, biyo bayan gardama daga ɓangarorin biyu.

People are also reading