Home Back

Mafi Ƙarancin Albashi: Ƙungiyar Ƙwadago Ta Yi Fatali Da Tayin Gwamnatin Tarayya Na ₦62,000

leadership.ng 2024/7/1
Mafi Ƙarancin Albashi: Ƙungiyar Ƙwadago Ta Yi Fatali Da Tayin Gwamnatin Tarayya Na ₦62,000

Ƙungiyar Ƙwadago ta bayyana cewa ba za ta sake tattaunawa kan tayin mafi karancin albashi na ₦62,000 da gwamnatin tarayya ta gabatar ba, inda ta bayyana shi a matsayin albashin zama da yunwa.

Ƙungiyar NLC da takwararta ta (TUC), sun yi gargadin cewa idan har gwamnatin tarayya da majalisar dokokin Nijeriya, suka gaza aiwatar da buƙatun ma’aikata zuwa ranar Talata, sassanta za su hadu domin yanke shawara kan batun dawo da yajin aiki a fadin ƙasarnan.

Mataimakin babban sakataren Ƙungiyar NLC, Chris Onyeka, wanda ya bayyana haka a wata hira da gidan Talabijin na Channels, safiyar yau Litinin, ya ce ma’aikata za su tashi tsaye idan wa’adin mako guda da aka bai wa gwamnatin tarayya a ranar Talata, 4 ga watan Yuni, 2024, ya kare a daren Talata, Yuni 11, 2024.

Da yake magana kan yiwuwar matakin Ƙungiyar Ƙwadago idan gwamnati ta dage a kan Naira 62,000, Onyeka ya ce, a bayyane yake abin da suka faɗa na sassauta yajin aikin da suka yi a fadin ƙasarnan, don haka rassan kungiyoyin kwadago za su yanke shawarar cewa ya kamata su janye wannan dakatarwar, hakan yana nufin su koma yajin aiki.

Ya jaddada cewa Ƙungiyar ƙwadago ba za ta karbi ₦62,000 ko ₦100,000 a matsayin albashi mafi ƙarancin ga ma’aikatan Nijeriya ba, inda ta dage a kan ₦250,000, kamar yadda Ƙungiyar Ƙwadago ta bukata a taron karshe na kwamitin mafi ƙarancin albashi a ranar Juma’a, a matsayin albashin ma’aikacin Nijeriya.

Ya ƙara da cewa haƙiƙanin gaskiya shi ne farashin kaya ƙara tashi ya ke a kowacce rana tare da bayar da misali da tashin kayan abinci da sauransu.

People are also reading