Home Back

Kotun Tarayya Na Shirin Yanke Hukunci Kan Halascin Mayar da Sarki Sanusi a Kano

legit.ng 2024/7/5
  • An fara shiga fargaba a Kano yayin da Babbar Kotun Tarayya ke shirin ynake hukunci kan halascin dokar sarauta da ta dawo da Sanusi II
  • A yau Alhamis, 20 ga watan Yuni, 2024 mai shari'a Muhammad Liman zai yanke hukunci a karar da Aminu Babba Ɗanagundi ya shigar
  • Mai karar ya nemi kotun ta soke dokar sarautar Kano kana ta dawo da Sarki na 15 Aminu Ado da sauran sarakuna huɗu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Babbar Kotun Tarayya mai zama a jihar Kano ta shirya yanke hukunci kan sabuwar dokar sarauta da ta dawo da Sarki Muhammadu Sanusi II.

Kotun karkashin jagorancin mai shari'a Muhammad Liman ta tsara yanke hukunci kan rigimar sarautar Kano a yau Alhamis, 20 ga watan Yuni, 2024.

Aminu Ado, Gwamna Abba da Sanusi II.
Yau Alhamis Babbar Kotun tarayya za ta yanke hukunci kan rigimar sarautar Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf, Imran Muhammad Asali: Twitter

Sarkin Dawaki Babba, Aminu Babba DanAgundi ne ya shigar da ƙarar gaban kotun yana ƙalubalantar tube Sarki na 15, Aminu Ado Bayero, Leadership ta ruwaito.

Tun da fari dai kotun ta yanke hukuncin cewa tana da hurumin sauraron ƙorafin take haƙƙin Mai Martaba Sarki Aminu Ado Bayero.

Waɗanda ake ƙara a shari'ar sun haɗa ɗa gwamnatin Kano, majalisar dokoki, kakakin majalisar dokoki da Antoni-Janar wanɗa shi ne kwamishinan shari'a na Kano.

Sauran sune kwamishinan ƴan sandan jiha, sufeta janar na kasa (IGP), hukumar tsaron fararen hula NSCDC da hukumar DSS.

A zamanta na karshe, Babbar Kotun Tarayya t asaurari jawaban kowane ɓangare kana ta sanya yau 20 ga watan Yuni a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan halascin rusa masarautu.

Idan zaku iya tunawa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya mayar da Muhammadu Sanusi II kan kargar sarauta bayan rusa masarautu biyar.

Hakan ta faru ne biyo bayan rattaba hannu kan dokar da ta tsige sarakunan da Abdullahi Ganduje ya naɗa tare da dawo da tsarin Sarki ɗaya a jihar Kano.

Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, wanda shi ne sarki a lokacin da aka yi wa dokar kwaskwarima, ya kalubalanci matakin da gwamnan jihar ya dauka.

A wani rahoton kun ji cewa

Asali: Legit.ng

People are also reading