Yajin Aiki: Akpabio da Abbas Sun Shiga Tattaunawar Gaggawa Da ’Yan Kwadago
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugabannin majalisar dokokin tarayya sun saka labule da 'yan kwadago domin yin wani taron gaggawa a daren yau.
Wannan ganawar na daga wani yunkurin da 'yan majalisar ke yi na ganin 'yan kwadago ba su shiga yajin aikin da suka dauri aniyar farawa a gobe Litinin ba.
Shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero da Festus Osifo na TUC ne suka wakilci 'yan kwadago a wannan taron, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas ne suka wakilci bangaren majalisar majalisar dokokin tarayya.
Majalisar dokokin kasar ta ce taron na da nufin "hana 'yan kwadago fara yajin aikin" da za su fara ranar Litinin, 3 ga Yuni, 2024, "wanda zai yi tasiri ga jama'a da tattalin arziki".
Matakin da kungiyar kwadagon ta dauka ya biyo bayan rashin maslahar da aka samu tsakaninta da gwamnatin tarayya kan sabon mafi karancin albashin ma’aikata.
Haka zalika, kungiyar ta nemi gwamnatin tarayya da ta janye karin kudin wutar lantarki da ta yi a baya wanda har yanzu ba a janye ba.
A ranar Juma’a ne kungiyar kwadago ta ayyana shiga yajin aikin saboda kin amincewa da gwamnatin tarayya ta yi na kara karin mafi karancin albashin ma’aikata.
Jaridar The Punch ta ruwaito 'yan kwadagon sun ki amincewa da tayin gwamnati har sau uku kan karin mafi karancin albashin, na baya-bayan nan shi ne N60,000.
Daga baya TUC da NLC suka fice daga tattaunawar, inda suka dage a kan ₦497,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi ga ma'aikatan kasar.
A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan Najeriya na kwankwadar akalla lita biliyan 1.6 ta madara a duk shekara yayin da gwamnati ke kashe $1.5bn wajen shigo da ita.
Karamin ministan noma da samar da abinci, Sanata Aliyu Abdullahi ya bayyana hakan a taron bikin ranar madara ta duniya ta 2024.
Asali: Legit.ng