Home Back

Iran: Dubban jama'a sun halarci sallar gawar Raisi

dw.com 2024/6/29
Iran | Trauer um Ebrahim Raisi
Hoto: Tasnim Agency

Dubun dubatar al'ummar Iran sun yi dandazo da sanhin wannan safiya ta Laraba a birnin Teheran domin girmama shugaban kasar marigayi Ebrahim Raisi da tawagar da ke marasa a lokacin da Allah ya karbi ransu a yayin hatsarin jirgi mai saukar Ungulu a ranar Lahadin da ta gabata.

Masu aiko da rahotanni sun ce jama'ar sun taru a jami'ar birnin Teheran inda jagoran juyin juya hali Musulumci Ayatullahi Ali Khameni ya jagoranci addu'o'in bankwana ga marigayi Ebrahim Raisi wanda ya mutu yana da shekaru 63 a duniya da kuma sauran manyan jami'an gwamnatin kasar da suka rasu tare da shi.

Ana sa ran wakillan kasashe da dama za su halarci jana'izar marigayi Raisi ciki har da wakilan Rasha da Turkiyya da kuma Iraki, sannan kuma shugaban Hamas Ismail Haniyey da mataimakin shugaban Hizbullah Naim Qassem suma za su kasance daga cikin wadanda za su mahalarci jana'izar.

People are also reading