Home Back

Ranar ma'aikata: Najeria ta kara albashin ma'aikata

dw.com 2024/5/17
Hoto: Emmanuel Osodi/AP Photo/picture alliance

Gwamnatin tarayyar Najeria ta sanar da karin albashin ma'aikata da kashi 25 da kuma kashi 35 cikin 100, wanda zai yi waiwayen komawa tun watan Janairun da ya gabata don fara cin gajiyarsa, a daidai lokacin da al'ummar kasar ke fuskantar tsananin rayuwa mafi muni a cikin shekaru 30.

Wannan na cikin wata sanarwa da hukumar kula da albashin kasar ta fitar, tana mai cewa karin albashin ya shafi dukkan ma'aikatan gwamnatin tarayya, da suka hada da jami'an tsaro da na lafiya da kuma na ilimi.

Mafi karancin albashin ma'aikata a duk wata ya kama naira 37,500, a shekara kuma naira 450,00 daidai da Dalar Amurka 323.97.

Hauhawar farashi a Najeriya ya kai kashi 33.20 cikin 100, kuma shi ne mafi tsanani a cikin shekaru 28, bayan da gwamnatin kasar ta janye tallafin man fetur da kuma yadda darajar Naira ke ci gaba da faduwa kasa wanwar.

People are also reading