Home Back

Yan baro a kasuwar sabon gari sun gudanar da zanga – zangar lumana a titin gidan gwamnati.

dalafmkano.com 2024/5/17

Ƙungiyar ƴan baro dake kasuwar sabon gari a jihar kano, sun gudanar da zanga-zangar lumana akan titin gidan Gwamnatin jihar Kano, inda suke zargin shugabancin kasuwar da tilasta musu tashi daga guraren da suke gudanar da kasuwancin su a kasuwar, lamarin da hakan ke barazana da rayuwar su.

Shugaban ƙungiyar Tasi’u Ibrahim, ne ya jagoranci zanga-zangar lumanar a yau Laraba, inda suke kira ga mahukunta wajen duba halin da za su shiga idan har aka tilasta musu tashi daga kasuwar sabon garin a wannan lokaci, inda suka ce sun kwashe tsawon lokaci suna gudanar da kasuwancin su a nan amma sai gashi lokaci guda an hanasu.

Da yake nasa jawabin jim kaɗan bayan zanga-zangar lumanar shugaban kasuwar ta Sabon Gari Alhaji Abdul Bashir Hussain, ya ce ana yawan samun matsala da yawaitar korafe – korafe akan yan baron wanda hakan tasa shugabancin kasuwar ya zauna da masu ruwa da tsaki daga ciki harda jami’an tsaro domin shawo kan lamarin.

Abdul Bashir ya kara da cewa akwai wani tsari da shuagabancin kasuwar ya yiwa ƴan baron na sama musu makoma, wanda hakan zai kawo karancin samun cinkoso a cikin kasuwar ta sabon gari.

People are also reading