Home Back

Atletico Madrid na son Alvarez, idon Galatasaray na kan Martial

bbc.com 2024/10/5
Anthony Martial

Atletico Madrid ta tuntubi ƴan ukun Argentina, wato Angel Correa, Rodrigo de Paul da kuma Nahuel Molina, a kan ɗan wasan, gaba na Manchester City Julian Alvarez mai shekara 24. (Marca - in Spanish), external

Paris St-Germain ma na son Alvarez. (Fabrizio Romano)

Manchester United ta bi takwararta Liverpool a son dan wasan tsakiya na Faransa Leny Yoro from Lille mai shekara 18. (Marca - in Spanish)

Sai dai da alama ba lallai Manchester United ta samu dan wasan ba, yayin da Real Madrid ke sahun gaba kan dauko dan wasa Yoro. (Mail)

Manchester City ta shirya tsaf domin tattaunawa da kociyanta Pep Guardiola, mai shekara 53, kan makomarsa. (Telegraph - subscription required)

Galatasaray na son dauko dan wasan gaba na Faransa Anthony Martial, mai shekara 28, sai dai dole ya rage bukatun da ya gabatar idan ya bar kungiyar Manchester United. (ESPN)

Tottenham ta bi takwararta Aston Villa a son kashe fam miliyan 50 a ƙoƙarin ɗauko dan wasan tsakiya na Ingila mai taka leda a Chelsea Conor Gallagher, mai shekara 24, wanda ita ma Atletico Madrid ke son dauka. (Mail)

Kungiyar Besiktas ta kasar Turkiyya ta duba yiwuwar ɗaukar tsohon manajan Manchester United Ole Gunnar Solskjaer, kafin su ɗauko kociyan Rangers Giovanni van Bronckhorst. (ESPN)

Barcelona na son dan wasan tsakiya na Sifaniya, mai taka leda a Real Sociedad Mikel Merino, mai shekara 27. (Sport - in Spanish)

People are also reading