Home Back

YUNƘURIN ƁALLEWA DAGA NAJERIYA: Yarabawa sun fi sauran ƙabilu samun dama a Najeriya a gwamnatance, tun daga 1999 zuwa yau – PREMIUM TIMES

premiumtimesng.com 2024/5/4
YUNƘURIN ƁALLEWA DAGA NAJERIYA: Yarabawa sun fi sauran ƙabilu samun dama a Najeriya a gwamnatance, tun daga 1999 zuwa yau – PREMIUM TIMES

A wani zazzafan ra’ayi da PREMIUM TIMES ta wallafa safiyar Litinin, ta yi kakkausan suka ga wani gungun Yarabawa masu hanƙoro da ƙumajin neman kafa ƙasar Yarabawa.

Gungun waɗanda jami’an tsaro suka tarwatsa tare da kama wasu da dama a mokonni biyu da suka gabata a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, sun nemi kafa ƙasar Yarabawa zalla ne.

PREMIUM TIMES ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya a gaggauta hukunta duk mai hannu a cikin wannan yunƙuri, kuma a nemi Amurka ta kama wadda ta ce matar marigayi MKO Abiola ce, da ke zaune Amurka, da ta ayyana ita ce ke ɗaukar nauyin su.

Cikin ra’ayin na PREMIUM TIMES, jaridar ta tunatar cewa, idan ma wani yanki ko wata ƙabila ya yi ƙorafin ana maida shi saniyar-ware a mulkin Najeriya, to ƙabilar Yarabawa ba su da wani dalilin da zai sa su fito su na wani ƙorafi.

Jaridar ta ce tun daga mulkin Obasanjo farkon 1999, Yarabawa ne suka fi cin moriyar dimokraɗiyya a ƙasar nan.

“Olusegun Obasanjo (Bayarabe), ya yi mulki shekara takwas daga 1999-2007; Yemi Osinbajo (Bayarabe), ya yi Mataimakin Shugaban Ƙasa daga 2015-2023. Yanzu kuma ga Tinubu (Bayarabe), wanda yanzu mulkin Najeriya a hannun sa yake.

“Kuma a yanzu dukkan hukumomin da ke kula da shigowar kuɗaɗe aljihun gwamnati, a hannun Yarabawa suke: Irin su Ma’aikatar Fetur, CBN, Ma’aikatar Harkokin Kuɗaɗe, Hukumar Kwastan, Ofishin Akanta Janar da sauran manyan Ma’aikatu da Hukumomi waɗanda su ne jini, jiki da jijiyar gwamnati.”

People are also reading