Home Back

Abin Da Ke Dagula Rashin Tsaron Nijeriya – Babban Hafsan Sojin Sama

leadership.ng 2024/7/1
Abin Da Ke Dagula Rashin Tsaron Nijeriya – Babban Hafsan Sojin Sama

Babban hafsan hafsa sojin sama, Air Marshal Hasan Abubakar ya danganta fafatawar da ake yi a tsakanin kasashen Amurka, Rasha da China a nahiyar Afirka, da kuma janyewar sojojin Jamhuriyar Nijar daga cikin rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa, a matsayin lamarin da ya kara ta’azzara kalubalen tsaro a yankin Sahel wanda ya haifar da kwararar makamai da ‘yan ta’adda zuwa Nijeriya.

Air Marshal Abubakar ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin wata ganawa da hafsoshin reshe da kwamandojin rundunar sojin sama da daraktoci da kuma daukacin manyan jami’an rundunar sojin saman Nijeriya a Abuja.

Da yake jawabi a wajen taron wanda ya zo daidai da shekara guda da ya yi a kan karagar mulki, Air Marshal Abubakar ya ce yakin Rasha da Ukraine ya hana NAF samun kayyakin jiragen sama da kuma kula da jirage masu saukar ungulu na Mi-series wadanda ke da matukar muhimmanci a ayyukanta na yaki da ta’addanci.

“Yayin da Nijeriya ke fuskantar kalubalen tsaro, kasar Amurka ta ba da goyon baya wajen sayen jiragen sama da makamantansu domin yaki da ta’addanci. Hakazalika, sojojin saman Nijeriya sun samu jiragen sama da alburusai daga kasashen China da Rasha kuma suna ci gaba da yin hadin gwiwa a fannin soji. Daidaita wadannan alakoki na da matukar muhimmanci ga muradun tsaron Nijeriya”.

Ya kara da cewa harin da Hamas ta kai kan Isra’ila a ranar 7 ga Oktoba 2023 da kuma hare-haren da ‘yan tawayen Houthi ke kaiwa kan layukan jiragen ruwa ta tekun Bahar Maliya sun kuma yi “mummunan tasiri wajen samun fasahohin zamani da ake yayi kamar jiragen sama marasa matuka, da sadarwar tauraron dan adam da kuma kirkirarriyar basira ta AI.”

Ya kuma kara da cewa karuwar juyin mulki da kuma ficewar kasashen Burkina Faso da Mali da Nijar daga kungiyar ECOWAS na da mummunar tasiri ga tsarin tsaro na yankin bai-daya a tsakanin Nijeriya da kasashen.

Ya yi nuni da cewa, hukumomin sojan kasar sun koma kasar Rasha domin neman taimakon tsaro, sakamakon gazawar kungiyar ECOWAS wajen magance tashe-tashen hankulan masu ikirarin jihadi a kasashen. .

“Bugu da kari, janyewar dakarun Majalisar Dinkin Duniya daga MINUSMA, da sojojin Chadi 2000 daga Mali, da kuma sojojin Jamhuriyar Nijar daga cikin rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa, na iya kara tsananta kalubalen tsaro a yankin Sahel, lamarin da ya haifar da kwararar makamai da ‘yan ta’adda. A ko da yaushe, wannan lamarin yana kawo cikas ga kokarinmu na yaki da ta’addanci.”

Ya yi gargadin cewa, “Saboda haka, da alama za mu shaida karuwar irin barazanar da aka fuskanta a baya. Don haka, ba wani riba ba ne, dole ne mu himmatu tare da kara himma wajen cimma burin gwamnatin Tarayya da ‘yan Nijeriya na samun wani mataki da zai kai mu ga samun nasara.

Sai dai kuma ya bayyana cewa NAF a cikin watanni 12 da suka gabata ta samu gagarumin ci gaba wajen yaki da ta’addanci, da ‘yan fashi, da masu satar mai da sauran ayyukan miyagun laifuka a kasar nan.

“Duk da haka, akwai sauran abubuwa da yawa da za a yi. Halin da ake ciki na matsin tattalin arziki – yawan rashin aikin yi na matasa, karuwar hauhawar farashin kayayyaki da kuma yawan talauci sun kara dagula yanayin tsaro a kasar. Don haka, dole ne mu yi wannan taron don samun nasara duba da yadda muka gudanar da ayyukanmu a cikin watanni 12 da suka gabata wajen kawo sauyi ga rundunar sojin saman Nijeriya domin biyan bukatun tsaron Nijeriya yadda ya kamata,” in ji shi.

People are also reading