Home Back

'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Farmaki Kan Bayin Allah, Sun Kashe Jami'an Tsaro

legit.ng 2024/7/2
  • Yan bindiga sun kashe ɗan sanda da ƴan banga a Kakangi da ke ƙaramar hukumar Burnin Gwari a jihar Kaduna
  • Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kuma yi garkuwa da manoma da dama suna tsaka da aiki a gonakinsu ranar Lahadi
  • Jami'in hulda da jama'a na rundunar ƴan sandan Kaduna, ASP Mansir Hassan ya ce jami'an tsaro sun daƙile harin tare da kashe ƴan bindiga da dama

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Wasu ƴan bindigan daji sun kai farmaki gundumar Kakangi da ke yankin ƙaramar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Maharan sun kashe ƴan banga huɗu da ɗan sanda ɗaya yayin harin na ranar Lahadi, 23 ga watan Yuni, 2024.

Malam Uba Sani.
Yan bindiga sun tafka ɓarna a karamar hukumar Birnin Gwari Hoto: Senator Uba Sani Asali: Twitter

‘Yan bindigar sun kuma yi awon gaba da wasu mutane da dama da ba a tantance adadinsu ba a kusa da wata gona da ke unguwar Sabon Layi a wannan gunduma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yahaya Musa Dan Salio, mamba mai wakiltar Kutemeshi a majalisar dokokin jihar Kaduna, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Daily Trust ranar Litinin.

“Eh, daga cikin wadanda aka kashe akwai ‘yan banga na yankin da kuma wani mutum daya da ‘yan bindigar suka kashe ranar Lahadi.
"Akwai kuma wasu mutanen kauyen da aka sace a gonakinsu da ke kusa da Sabon Layi, duk a karkashin mazabata.”

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan ya tabbatar da kai harin da kuma asarar rayuka.

"A lokacin da muka samu labarin cewa ‘yan bindiga sun kai wa mutane hari a gonakinsu, DPO na ‘yan sanda da mafarauta suka haɗu suka daƙile harin."
"Yayin musayar wuta ne ƴan banga uku da ɗan sanda ɗaya suka rasa rayuwar su, sannan an kashe ƴan bindiga da dama sauran kuma sun tsere da raunuka a jikinsu," in ji shi.

An kashe mutane a Katsina

A wani rahoton kun ji cewa Ƴan bindiga sun kai mummunan hari garin Maidabino da ke ƙaramar hukumar Ɗanmusa a jihar Katsina, sun kashe bayin Allah.

Mazauna garin sun bayyana cewa yawan ƴan bindigar ya sa babu jami'in tsaron da ya iya tunkararsu, sun kuma tafi da mutane 50.

Asali: Legit.ng

People are also reading