Home Back

Jihar Gombe Ta Rusa Kamfanin Zuba Jari Da Bunƙasa Ƙadarori

leadership.ng 2024/7/29
Jihar Gombe Ta Rusa Kamfanin Zuba Jari Da Bunƙasa Ƙadarori

Majalisar Zartarwar Jihar Gombe ƙarƙashin jagorancin Gwamna Mahammadu Inuwa Yahaya ta amince da rusa Kamfanin Zuba Jari da Bunƙasa ƙadarori na Jihar Gombe, GIPDC. 

Kwamishinan kuɗi da bunƙasa tattalin arziƙi, Malam Muhammadu Gambo Magaji, ne ya sanar da hakan, yana mai cewa an ɗauki matakin ne don daidaitawa da ƙarfafa hukumomin zuba jari na jihar.

“Bayan nasarar da aka samu a babban taron zuba jari na Gombe na 2022 da kuma burinmu na karɓar baƙuncin wani taron na gaba da za a yi a watan Oktobar bana, tare da ci gaba da riƙe kambunmu na jagora a fagen sauƙaƙa kasuwanci, gwamnati ta ɗauki wani tsari mai inganci na ƙarfafa hukumomin zuba jari da kuma magance kashe-kashen kuɗaɗe ba gaira ba dalili da ma kawo ƙarshen maimaita ayyuka”

Kwamishinan ya ƙara da cewa, “Duba da yadda Kamfanin Zuba Jari da Bunƙasa Kadarorin na Jihar Gombe da Kamfanin Haɓaka Kuɗaɗen Shiga na jihar suke aiki iri ɗaya, majalisar zartarwar ta yanke shawarar rushe kamfanin zuba jari da bunƙasa kadarorin na jiha (GIPDC) da nufin daidaita ayyukansa da rage kashe-kashen kuɗi dama inganta aiki”.

Ya ce za a mayar da ayyukan kamfanin zuwa wasu hukumomin da abin ya shafa, “Kamfanin Haɓaka kuɗaɗen shiga da bunƙasa kadarorin zai koma GROCOL, sannan za a mayar da ɓangaren bunƙasa gidaje ga Ma’aikatar Gidaje ta Jihar Gombe, kuma nan ba da daɗewa ba Gwamna zai naɗa shugabannin da za su jagoranci hukumar, za a mayar da harkokin kasuwanci da zuba jarin da GIPDC ke da su ga kamfanin Gombe State Security Company Ltd da ya zama kufai”

Hon. Gambo Magaji ya jaddada cewa matakin ba zai shafi ma’aikatan kamfanin ba ta kowace fuska, yana mai cewa za a sake fasalin hukumar gudanarwar ta yadda za a samu sauƙin gudanar da ayyuka masu inganci.

People are also reading