Home Back

Ni Na Yi Ruwa Da Tsaki Har Ali Nuhu Ya Samu Shugabancin Hukumar Fina-finai Ta Nijeriya – Rarara

leadership.ng 2024/4/28
Ni Na Yi Ruwa Da Tsaki Har Ali Nuhu Ya Samu Shugabancin Hukumar Fina-finai Ta Nijeriya – Rarara

Shahararren mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, ya bayyana cewa, shine da kansa ya shiga ya fita har sabon shugaban hukumar Fina-finai ta Nijeriya, Ali Nuhu ya samu wannan mukami.

Rarara ya bayyana haka ne a yayin da yake amsa tambayoyin yan jarida, inda ya kara da cewa, yayi matukwar farin ciki da Ali Nuhu ya samu wannan mukami.

Da yake amsa tambayoyin yan jarida akan ko gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu wadda yayi ikirarin kafawa ta biyashi aikin da yayi mata a lokacin yakin neman zabe ta hanyar nada amininsa kuma jarumi Ali Nuhu matsayin shugaban hukumar Fina Finai ta Nijeriya?

Rarara ya amsa da cewa, “ko kusa wannan abu da aka yi wa Ali Nuhu ba shine zai nuna an biya ni aikin da na yi wa shugaba Bola Ahmed Tinubu ba, duk da cewa naji dadi sosai akan wannan mukami da Ali Nuhu ya samu amma wannan bai zama dalilin da zai sa ace an biyani ba.”

 
People are also reading