Home Back

Abincin Da Ke Haifar Da Ciwon Mara Lokacin Al’ada

leadership.ng 2024/5/5
Abincin Da Ke Haifar Da Ciwon Mara Lokacin Al’ada

Assalamu alaikum masu karatu, barkammu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Ado Da Kwalliya.

Da dama dai a bangaran lafiya abin da muke dauka ba komai ba zai iya haifar mana da damuwa ko kara tsananta wani hali ko yanayin da muke ciki.

A bangare al’ada da dama mata kan hadu ko ji alamun ciwon mara lokacin da suke al’ada, ko kafin su fara.

Matukar mace za ta rika amfani da su to akwai yiyuwar karuwar matsalar ciwon mara.

Chacolate, Suga ko abu mai suga, Coffee, Dairy foods, wato kamar ire- iren madara, Processed food wato kamar abincin da za’a sarrafa kamar abincin gwangwani, Fatty food wato kamar abu mai kitse, Salty food, wato kamar abu mai gishiri da dai ssuransu.

Matukar mace za ta rika amfani da kowane nau’in abinci mai dauke da wadannan kalar abincin da muka ambata to matsalar za ta iya karuwa.

Zafin ciwo na mahaifa na daga cikin dalili mafi kusa da ke sa mata jin ciwon mara a lokacin al’ada.

People are also reading