Home Back

Jami'an tsaro sun tarwatsa masu Sallar Idi a Nijar

rfi.fr 2024/5/2

Jami'an Jandarma a Jamhuriyar sun tarwatsa masu Sallar Idi yau Laraba a garin Baruwana tare da cafke Limamin da ya bada Sallar.

Wallafawa ranar: 10/04/2024 - 19:55

Minti 1

Taswirar wasu yankunan Jamhuriyar Nijar.
Taswirar wasu yankunan Jamhuriyar Nijar. © Wikipedia

Bayanai sun ce mutane da dama suka jikkata yayin aukuwar lamarin, yayin da daruruwan yara sun ɓace, sakamakon rikicewar da suka yi saboda shakar barkonon tsohuwa.

Akwai dai mutane da dama a Maradi da a yau ne suka gudanar da ta su Sallar ta Idi.

Malam Abdullahi na cikin wadanda suka arce bayan sun sha barkonon tsohuwar da jami'an tsaro suka harba.

Malam Abdullahi ɗaya daga cikin mutanen da jami'an tsaro suka watsa bayan gudanar da Sallar Idi a ranar Laraba

A ranar Talata 9 ga watan Afrilun ne dai akasarin al'ummar Jamhuriyar Nijar suka gudanar da Sallah Karama bayan sanar da ganin jinjirin watan Shawwal da mahukuntan kasar suka yi a ranar Litinin.

Bayanai sun ce mahukuntan na Nijar sun tabbatar da ganin jinjirin watan na Shawwal ne a jihohi akalla biyar da ke fadin kasar, abinda ya sanya suka bayyana Talata 9 ga watan Afrilu a matsayin ranar Sallah wadda tayi daidai da 1 ga watan Shawwal shekara ta 1445.

Sai dai akasarin kasashen Musulmi sun gudanar da Sallar Idin karama ce a ranar Laraba, bayan cika kwanaki 30 na watan Ramadan.

People are also reading