Kungiyar Kwadago Ta Hana Alkalai Zaman Kotu Saboda Yajin Aiki a Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja - Kungiyar ma'aikatan kotu (JASUN) ta hana zaman kotu a birnin tarayya Abuja biyo bayan fara yajin aikin 'yan kwadago.
A safiyar yau Litinin ne kungiyar ta kulle kotuna domin hana alkalai, lauyoyi da masu ƙara shiga su gabatar da shari'a.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar JASUN ta dauki matakin ne a kusan dukkan kotunan da suke birnin Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan kungiyar JASUN sun yi zaman dirshan yayin da suka kulle babban kotun kasa da ke Abuja a yau.
Ma'aikata sun hana alkalai, lauyoyi, masu shigar da ƙara, masu ziyara da 'yan jarida shiga kotun domin yin ayyuka, rahoton Vanguard.
Ma'ajin JASUN, Muhammad Danjuma-Yusuf ya ce kotuna 20 da suke karkashin kotun daukaka kara duk an kulle su a yau.
Muhammad Danjuma-Yusuf ya ce ba su bar kowa ya shiga kotunan ba kuma haka lamarin zai cigaba har sai kungiyar kwadago ta janye yajin aiki.
Shugaban kungiyar JASUN reshen Abuja, Samuel Ikpatt ya ce kungiyar ta bi umurnin kungiyar kwadago ne wajen rufe kotunan a yau.
Samuel Ikpatt ya ce ba su bar wani ya shiga kotun domin aiki ba kuma sun tabbatar da haka a dukkan kotunan da ke birnin Abuja.
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sandan Najeriya ta gargadi kungiyar kwadago kan shiga yajin aiki da ta yi a yau Litinin.
Rundunar 'yan sandan ta ce yajin aikin ba bisa doka da oda yake ba kuma zai iya kai ga tayar da fitina a Najeriya saboda haka ya kamata kungiyar kwadago ta gaggauta janye sa.
Asali: Legit.ng