Home Back

Kotu ta samu Donald Trump da laifukan tuhume-tuhume 34 da ake masa

bbc.com 2024/7/3
Donald Trump

Asalin hoton, Getty Images

Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, ya zamo shugaban Amurka na farko da za a yankewa hukunci a kan tuhuma ta mugun laifi, bayan da masu taimaka wa alkali yanke hukunci suka same shi da laifi a tuhume-tuhume 34 da ake yi masa.

Dukkan tuhume-tuhumen na da alaka da karyar da ya yi a harkokin kasuwancinsa domin boye kudin da ya bayar na toshiyar baki a kan alakarsu da mai fitowa a fina-finan batsa wato Stormy Daniels a lokacin gangamin yakin neman zaben shugaban kasar a 2016.

Da yake Magana a wajen kotun da ke Manhattan bayan samunsa da laifi, Donald Trump, wanda za a yankewa hukunci a watan Yuli mai zuwa, ya kira sakamakon zaman da aka yi a matsayin an yi masa almundahana da coge kuma hakan wani babban aibune.

Sannan ya kara da cewa al’umma za su yanke hukunci na gaskiya a ranar zabe mai zuwa a watan Nuwamba.

Tuni dai shugaba Biden ya yi maraba da sakamakon shari’ar ta ranar Alhamis, ya na mai cewa ba wanda ya fi karfin doka.

Kazalika a wata sanarwa da kwamitin yakin neman zabensa ya fitar, ya jaddada cewa, a matsayin mutumin da ake ganin zai yi wa jam’iyyar Republican takara a watan Nuwamba, Donald Trump, zai ci gaba da kasancewa babbar barazana ga dimokradiyya, sannan ya zarge shi da kara kambama aniyarsa ta kullata da neman yin ramuwar gayya.

Sabanin haka, shugaban majalisar wakilai ta Amurka, Mike Johnson, ya kira zaman kotun a matsayin abin kunya da alawadai ga Amurka, sannan ya ce Trump zai daukaka kara.

People are also reading