Home Back

Falalar Ziyarar Kabarin Annabi S.A.W (1)

leadership.ng 2024/6/29
Falalar Ziyarar Kabarin Annabi S.A.W (1)

Ziyarar kabarin Manzon Allah (SAW) tana daga cikin ibadu mafi girma da samun kusanci zuwa ga Allah (SWT). Babu wata ibada da ta kai darajar Manzon Allah (SAW) a wurin Allah. Babu wani abu da Musulmi zai yi Allah ya ji dadi (yadda ya dace da shi SWT) kamar girmama Masoyinsa Manzon Allah (SAW). Domin girmama Manzon Allah, girmama Allah ne da ya aiko shi. Kuma ziyararsa (SAW), tana daga cikin girmama shi.

An karbo Hadisi daga Ummul-Mu’umina Aisha (RA) cewa Manzon Allah (SAW) ya ce, “Ni ne cikamakon Annabawa, Masallacina ne cikamakon Masallatan Annabawa, shi ne mafi cancantar Masallacin da za a daura kaya musamman don ziyartarsa.”

A nan, ba ana nufin cewa a ziyarci Masallacin ne muradi ba kawai, domin ai Masallacin ya daran ma sauran Masallatau ne saboda kasancewarsa na Manzon Allah (SAW).

Hatta mu kanmu wannan al’ummar, mun samu darajojin da muka samu ne saboda kasancewarmu al’ummar Annabi (SAW). Allah ya saka wa Shehu Ibrahim Inyass da alheri, wanda ya ce “girman bawa, daidai girman ubangidansa ne.

Dukkan darajoji da martabobin da Allah ya baiwa Annabawa, ya tara wa Annabi (SAW) kuma ya kara ma sa da wasu na daban.

Idan aka dubi wannan, bai kamata a rika bata karatu ana cewa Masallaci ne za a ziyarta amma ba Annabi (SAW) ba. Ya kamata a gyara karatu, a gyara wannan fahimtar. Saboda irin wannan fahimtar ce ta haifar da a zamanin nan an samu rashin girmama Manzon Allah (SAW) har aka dasa bom kusa da shi. Ko daga murya Allah ya hana a yi a gaban Annabi (SAW), to ina ga tada bom?

A hudubar sallar Idil Fidir da Limamin Makka ya yi a Harami, ya ce Yahudawa ne suka tada bom din, amma sai ga shi da Saudiyya ta nuna wanda ya yi abin, da sunanshi da kamanninsa har da dogon gemu, dan kasar ne mai ikirarin bin Salafiyya Sunnah. Duk ire-iren karatuttukan nan ne na rashin ganin girman Annabi (SAW) suke jawo wadannan bala’o’in. Ya kamata a ji tsoron Allah a gyara.

Malamai Malikawa sun yi hukuncin cewa zuwa ziyara a Madina wajibi ne ga wanda yake da hali. Ma’ana idan mutum ya yi Aikin Hajji, wajibi ne ya ziyarci Manzon Allah (SAW) idan yana da halin zuwa.

Masu cewa idan mutum ya yi Hajji shikenan ba sai ya tafi ziyarar ba, suna nuna alama ce ta kin Manzon Allah (SAW).

Hadisai masu yawa sun yi bayani a kan falalar ziyarar Manzon Allah (SAW).

Yana daga ciki, Abdullahi bin Umar (RA) ya ruwaito cewa, Manzon Allah (SAW) ya ce, “Duk wanda ya yi Hajji, sai ya ziyarci kabarina bayan mutuwata, ya zama kamar wanda ya ziyarce ni ne lokacin da nake da rai.” Ma’ana duk daya suke.

Askalani, mai sharhin Bukhari ya ce zuwa Madina iri biyu ne, ana zuwa a lokacin da Manzon Allah (SAW) yake raye a kan kasa domin a karbi shiriya, bayan wafatinsa kuma a je a ziyarci kabarinsa (SAW).

Dukkanin malamai na Allah Ahlus Sunnah tun daga kan Sahabbai a kan wannan fahimtar suke.

Haka nan, Hadisi ya tabbata daga Abdullahi bin Umar (RA) cewa, Manzon Allah (SAW) ya ce, “Duk wanda ya ziyarci kabarina, cetona ya cancanta a gare shi”. Abu Haraira (RA) ya ruwaito Hadisi daga Manzon Allah (SAW) ya ce, “Babu wani mutum da zai yi sallama a gare ni, face Allah ya dawo mun da raina har na amsa sallamar.”

Idan mutum zai je ziyarar, walau Alhaji ko wanda ba Alhaji ba, zai yi niyyar cewa zai je ya ziyarci Manzon Allah (SAW), sannan ya yi sallah a Masallacinsa, ya ziyarci sauran Sahabbai da wuraren Musulunci. Amma dai Annabi (SAW) ne a kan gaba.

Ana so idan mai ziyara ya tasam ma Madinar Annabi (SAW), ya yawaita salati ga Manzon Allah (SAW) domin ya kara samun haske da soyayyarsa (SAW).

Haka nan, ana so mutum ya yi wanka, ya sa turare, ya sa tufafinsa mafi kyau, kuma ya jaddada tubansa, sannan ya halarto da girman Annabi (SAW) a cikin zuciyarsa, da girman Sahabbansa, da ganin girman garin baki daya (a matsayin wurin da Annabi (SAW) da Iyalansa da Sahabbansa suka rayu, da faruwar abubuwan tarihi na Musulunci. Lallai idan mutum ya yi haka, zai ji wani karin imani har ya sa shi kuka.

Idan mai ziyara ya zo shiga Masallacin Annabi (SAW), ana so ya shiga da kafar dama ya ce “A’uzubillahil azim wa bi wajhihil karim wa suldanihil kadim minas shaidanir rajim, bismillah, allahumma salli ala Muhammadin wa alihi wa sallim, allahummagfirli zunubi waftahali abwaba rahmatika.”

Idan da hali ya yi kokari ya shiga Raula (wurin da Annabi ya ce Dausayin Aljanna ne) ya yi sallah nafila raka’a biyu a matsayin gaisuwar Masallaci. Idan kuma Raula ta cika, sai a yi sallar a duk wurin da aka samu a Masallacin.

Ana so idan mai ziyara ya tasam ma Madinar Annabi (SAW), ya yawaita salati ga Manzon Allah (SAW) domin ya kara samun haske da soyayyarsa (SAW).

Haka nan, ana so mutum ya yi wanka, ya sa turare, ya sa tufafinsa mafi kyau, kuma ya jaddada tubansa, sannan ya halarto da girman Annabi (SAW) a cikin zuciyarsa, da girman Sahabbansa, da ganin girman garin baki daya (a matsayin wurin da Annabi (SAW) da Iyalansa da Sahabbansa suka rayu, da faruwar abubuwan tarihi na Musulunci. Lallai idan mutum ya yi haka, zai ji wani karin imani har ya sa shi kuka.

Idan mai ziyara ya zo shiga Masallacin Annabi (SAW), ana so ya shiga da kafar dama ya ce “A’uzubillahil azim wa bi wajhihil karim wa suldanihil kadim minas shaidanir rajim, bismillah, allahumma salli ala Muhammadin wa alihi wa sallim, allahummagfirli zunubi waftahali abwaba rahmatika.”

Idan da hali ya yi kokari ya shiga Raula (wurin da Annabi ya ce Dausayin Aljanna ne) ya yi sallah nafila raka’a biyu a matsayin gaisuwar Masallaci. Idan kuma Raula ta cika, sai a yi sallar a duk wurin da aka samu a Masallacin.

Daga nan, idan lokacin ya kasance lokacin sallar farilla ne sai ya tsaya a kammala sallar, idan kuma ba lokacinta ne ba, yana idar da nafilar sai ya nufi ziyarar Annabi (SAW).

Idan ya zo wurin kabarin mai girma, sai ya baiwa alkibla baya; ya fuskanci bangon kabarin kusa da inda hukuma ta amince a tsaya. Ya halarto da girman Annabi (SAW) tare da tunanin cewa ga fuskar Annabi (SAW) tana kallonsa. Sai ya yi sallama cikin ladabi na sarari da boye, sannan ya yi salati ga Manzon Allah (SAW). Ma’ana ya ce”Assalamu alaika ya Rasulullah, assalamu alaika ya Nabiyyallah, assalamu alaika ya Khaira khalkillah, assallamu alaika ya Habiballah, assalamu alaika ya Sayyidal Murasalin, assalamu alaika ya rasula Rabbul alamin, assalamu alaika ya ka’ida gurril muhajjalin. Ash’hadu an la’ilaha illallah wa ash’hadu annaka abduhu wa rasuluhu wa aminuhu wa khiratuhu Wa ash’hadu annaka kad ballagtar risalata wa addaital amanata wa nasahtal ummata wa jahada fillahi hakka jihadihi.”

Sai mutum ya karanta ayar nan ta neman gafarar Allah a wurinsa (SAW) ta cikin Suratun Nisa’i. Idan ya samu hali sai ya dan ja baya kadan ya yi salati guda 70 ga Annabi (SAW).

Daga nan ya matsa daidai kamu daya a dama, ya yi sallama ga Sayyidina Abubakar (RA), kuma ya kara matsawa irin haka duk dai a dama, ya yi sallama ga Sayyidina Umar (RA). Daga nan sai ya fice ya kammala ziyara.

Dangane da juya wa albla baya a kalli fuskar Annabi (SAW) lokacin da mutum zai yi addu’a, an ruwaito cewa Abu Ja’afarul Mansur Al-Abbas (Sarkin Musulmi) ya tambayi Imam Malik (RA) da ya zo ziyara cewa, “Shin Annabi (SAW) zan fuskanta in yi addu’a ko alkibla?” Sai ya amsa ma sa da cewa “Don me za ka kawar da fuskarka ga Manzon Allah (SAW) alhali shi ne tsaninka kuma tsanin Babanka Adamu (AS) zuwa ga Allah?”. Saboda haka mai ziyara ya fuskanci Annabi (SAW) ya yi addu’a.

Amma da yake hukumar can ta yanzu ba su yarda a kalli Annabi (SAW) a yi addu’a ba, to sai mutum ya kalli Alkibla sai ya halarto da shi (SAW) a zuciya. Kuma koda ma alkiblar aka kalla dole sai an bi ta wurin Annabi saboda mutum zai yi salatinsa (SAW) a cikin addu’ar.

Akwai wasu da suke nuna wa Alhazai cewa ba koyaushe ne suka shiga Masallaci sai sun ziyarci Annabi (SAW) ba, suna kafa hujja da Hadisin da Annabi (SAW) ya ce “… kar ku sanya kabarina ya zamo wurin idi…”. A tasu fahimtar yin ziyararsa (SAW) koyaushe ya zama kamar Idi. To ba haka malamai suka fassara wannan Hadisin ba.

Ma’anar Hadisin in ji Malamai ita ce “kar a sanya ziyarar kabarin ta zama Idi wadda ba za a rika yi ba sai shekara-shekara.” Saboda dama Idi ba kullum ake yi ba, don haka Hadisin yana nufin kar a ki yin ziyarar har ya zama daga shekara sai shekara. Duk lokacin da aka samu iko a yi kawai.

Haka Malaman da ke da soyayyar Manzon Allah (SAW) a zuciyarsu suka fahimci Hadisin.

Bayan haka, ana so mai ziyara ya ziyarci makabartar Madina (Bakiy’ah Garkatu) yayin zamansa a can inda Sahabbai kimanin 10,000 ke kwance. ‘Ya’yan Manzon Allah (SAW) da Jikokinsa da Matansa duk suna kwance a wurin. Sai a ziyarce su a yi musu addu’a.

Kabarin Sayyidina Usman bin Affan (RA) yana nan a tsakiyar makabartar. Amma na Sayyidina Aliyu bin Abi Dalib, yana Kuhfa, Kasar Iraki. To amma duk da haka, an so a halarto da Sayyidina Aliyun a nan saboda wata ruwaya ta ce kila Sayyidina Hassan ya dauko shi zuwa nan Bakiy’a.

Daga nan, sai mutum ya ziyarci Uhudu (wurin da aka yi yakin Uhudu). Akwai kaburburan Shahidan Uhudu a nan ciki har da na shugaban Shahidai, Sayyidina Hamza (RA).

Haka nan, ana so a ziyarci Masallacin Kuba (farkon Masallacin da aka gina Manzon Allah (SAW) ya sauka kafin ya shiga Madina). Ana so a ziyarci Masallacin ranar Asabar, saboda Annabi (SAW) ya ce, “duk wanda ya yi wanka ya yi alwala ya ziyarci Kuba ranar Asabar, kamar ya yi Umura ne”. Ana so a yi nafila raka’a biyu a ciki, saboda Hadisin da Abdullahi bin Umar (RA) ya ruwaito cewa, “Manzon Allah (SAW) ya kasance yana zuwa Kuba a kan abin hawa ko da kafa duk ranar Asabar a duk zaman da ya yi a Madina.”

Sannan mai ziyara ya ziyarci farkon Masallacin da aka fara Jumma’a, watau Awadiyna Rauna’a. Sai Masallacin Alkibla guda biyu (Masjidu Kiblataini).

Daga nan sai ziyarar Khandag, wurin da aka yi yakin gwalalo har Annabi (SAW) ya yi wa Musulmi bisharar cewa za a kama Rum da Farisa da Yemen.

Duk da kamannin wuraren sun canza a yanzu, mutum ya yi kokari ya ziyarta domin albarkarsu tana nan ba ta gushe ba. Domin Annabi (SAW) ya ce duk wanda ya ziyarci Uhudu ko ‘yar ciyawa ce ta wurin ya tsinka ya ci.

Badar tana da nisa, amma idan Alhaji ya samu hali, nan ma ya yi kokari ya ziyarta.

Za mu ci gaba a mako mai zuwa, insha Allah…

People are also reading