Home Back

Tinubu Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Dawo Da Tsohon Taken Nijeriya

leadership.ng 2024/6/29
Tinubu Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Dawo Da Tsohon Taken Nijeriya

Shugaba Bola Tinubu, ya rattaba hannu kan kudirin dokar dawo da tsohon taken kasa na 2024, inda ya zama doka. 

Wannan na zuwa ne duk da rashin yarda da babban lauyan tarayya kuma ministan shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), ya yi na dawo da tsohon taken na Nijeriya.

Idan za a tuna a ranar Talata ne majalisar dattawa ta amince da dokar dawo da tsohon taken kasar nan, a wani yunkuri na dabbaka kishi a zukatan ‘yan Nijeriya.

Sai dai wasu ‘yan majalisar sun nuna takaicinsu kan wannan mataki da majalisar ta dauka.

Wannan doka ce da ‘yan majalisar suka ba ta muhimmanci da kuma hanzarta amincewa da ita a cikin kwanaki biyu kacal,

Shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawa, Okpeyemi Bamidele ne, ya dauki nauyin dokar dawo da tsohon taken Nijeriya, wanda ‘yan majalisar ke ganin harufan da aka yi amfani da su a cikin taken suna da ma’ana sosai kuma zai karfafa gwiwar al’ummar kasar nan wajen kaunar juna da hadin kai da kuma kyautata zamantakewa.

Sanata Rufa’i Hanga yana cikin masu wannan tunanin da ya ce tsohon taken Nijeriya waka ce da za ta kara karfafa kishin kasa a tsakanin ‘yan Nijeriya wadanda suka rayu cikin wannan zamanin, kuma sun fahimci muhimmiyar rawar da ta taka a tarihin al’ummarmu.

Hanga, ya ce taken Nijeriya da ake amfani da shi yanzu sojoji ne suka kawo shi kuma bai yi ma’ana kaman tsohon ba shi ya sa majalisa ta yi gaggawar amincewa da dokar saboda yaran wannan zamani su yi koyi da kalmomin taken domin ya sauya musu tunani.

Sai dai dan majalisar wakilai, Mohammed Shehu Fagge ya yi suka ne kan matakin da aka dauka na dawo da tsohon taken, inda ya yi tsokaci cewa, kawo wannan magana na sauya taken rashin sanin ciwon kai ne.

Shehu, ya ce a wannan hali da ‘yan kasa ke ciki na yunwa, fatara da rashi da sauran abubuwa makamantansu su ya fi dacewa a mayar da hankali a kai.

Shehu, ya ce shugabanin majalisa ba su yi tunani ba, domin ba shi ne abin da ‘yan kasa ke so ba.

Ya ce kamata ya yi a kalli dokoki da za su amfana wa talakan kasa da abubuwa da za su kawo wa rayuwarsu sauyi.

Shehu ya ce har yanzu majalisa ba ta kammala aiki kan kasafin kudin 2024 ba, saboda haka yana kira da a fuskanci bukatun al’umma.

Sai dai Sanata Mustapha Habib daga mazabar Jigawa ta Kudu, ya yaba da matakin da majalisa ta dauka, inda ya ce yana goyon bayan sauya taken, domin wakar da shi ya sani kenan tun yana yaro.

Habib ya ce taken yana da ma’ana kuma zai koyar da kishin kasa da kaunar juna.

Wannan tsohon taken Nijeriya dai wata baturiya mai suna Lillian Jean Williams ce, ta rubuta shi a lokacin da Nijeriya ta samu ‘yancin kai a 1960.

An daina amfani da taken ne a1978 bayan da aka samo wani sabon taken da wani dan Nijeriya mai suna Ben Odiase ya rubuta.

People are also reading