Home Back

HAJJ: ‘Yan majalisar dokokin Najeriya sun yaba wa NAHCON kan ciyar da maniyyata abinci da masauki masu kyau a kasar Saudiyya

premiumtimesng.com 2024/6/26
HAJJ: ‘Yan majalisar dokokin Najeriya sun yaba wa NAHCON kan ciyar da maniyyata abinci da masauki masu kyau a kasar Saudiyya

A ranar Talata ne wasu ‘yan majalisar dattawan Najeriya suka gudanar da aikin tantance wuraren kwana da kuma yadda ake ciyar da mahajjatan Najeriya a birnin Madina na kasar Saudiyya.

Ƴan majalisar karkashin jagorancin shugaban masu rinjaye na majalisar dattijai, Ali Ndume, sun ziyarci otal din mahajjata da dama domin ganin yadda ake ba su abinci.

Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala rangadin tantancewar, Sanata Ndume ya ce sun yanke shawarar gudanar da rangadin ne saboda nuna damuwa kan rashin ciyar da alhazan Najeriya da ake zargin hukumar Akhazai da yi.

Ya ce kafafen sada zumunta sun yi ta yawo da hotunan karya na rashin bada abinci mai kyau da ake yi wa alhazan Najeriya a Saudiyya.

Shima Sanata Sharafadeen Alli daga jihar Oyo, ya yabawa hukumar NAHCON bisa yadda take gudanar da wurin kwana da ciyarwar Alhazai da ta yi.

” Tsakani da Allah, abinda muka gani a ana rangaɗa wa mahajjatan Najeriya, ko ina ma sai haka. Abinci wuraren kwana, sam ba a nuna ƙaranta ba.” In ji Sanatocin Najeriya

Da yake ta sa jawabin Abubakar Yagawal, kwamishina a hukumar Alhazai na kasa, ya ce hukumar ba za ta yi ƙasa a guiwa ba wajen tabbatar da ganin an wadatar da alhazan Najeriya duk ababen da suke bukata na samun walwala da ji n daɗi a Makka.

People are also reading