Home Back

Gwamnati ta Yiwa Wasu 'Yan Najeriya Gata, An Dakatar da Karbar Haraji Daga Garesu

legit.ng 3 days ago
  • Gwamnatin tarayya ta dauko hanyar saukakawa kananan 'yan kasuwa da manoma ta hanyar dakatar da karbar haraji daga garesu
  • Shugaban kwamitin shugaban kasa a kan manufofin kasafin kudi da sauya fasalin haraji Taiwo Oyedele ne ya bayyana haka
  • Shugaban kwamitin ya kara da cewa an samar da sauye-sauye a fannin karbar haraji a kasar nan domin rage wadanda ke kin biyan haraji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja - Gwamnatin tarayya ta amince da dakatar da karbar haraji daga wasu 'yan Najeriya domin taimaka masu wajen gudanar da ayyuka.

Bangarorin da za za su mori tagomashin sun hada da manoma da masu kananan masana'antu a fadin kasar, a wani yunkuri na ganin an rage masu nauyi.

Bola Tinubu
Gwamnati za ta daukewa manoma, masu kananan masana'antu biyan haraji Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Asali: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa gwamnati ta amince da tsare-tsaren ne a wani yanayi na kawo sauyi cikin tsarin karbar haraji a kasa baki daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haraji: An samar da canje-canje a Najeriya

Shugaban kwamitin shugaban kasa a kan manufofin kasafin kudi da sauya fasalin haraji, Taiwo Oyedele ya ce gwamnati za ta sanya hannu kan daftarin dakatar da karbar haraji daga manoma da masu kananan masana'antu.

Channels Television ta wallafa cewa an yi sauye-sauye a tsarin karbar haraji a kasar nan domin saukakawa jama'a da rage karbar haraji mai yawa daga kananan 'yan kasuwa.

Daga cikin dalilan sauye-sauyen akwai rage yawan kananan masana'antu masu kin biyan haraji da rage haraji ga kasuwancin da ba sa samun kudi sosai.

"Biyan haraji zai amfani kasa," Kashim Shettima

A baya mun kawo labarin cewa gwamnatin tarayya ta ce biyan gwamnati haraji zai kawo ci gaba ga kasar nan, matukar aka dage da biya din.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya bayyana haka a taron kwamitin yiwa tattara haraji kwaskwarima, inda ya ce jihohi ma za su amfana.

Ya shaidawa 'yan Najeriya cewa an bijiro da karin karbar haraji ne domin kyautata rayuwarsu da gudanar da ayyukan raya kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

People are also reading