Home Back

'Yan Majalisa Sun Tsige Kakakin Majalisar Dokoki Saboda Wasu Zarge-Zarge

legit.ng 2024/9/28

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Cross Rivers - Ƴan majalisar dokokin jihar Cross Rivers sun tsige kakakin majalisar, Honorabul Elvert Ekom Ayambem daga muƙaminsa.

An tsige kakakin ne daga kan muƙaminsa a ranar Laraba, 22 ga watan Mayun 2024 bayan an zarge shi da yin watanda da kuɗade.

An tsige kakakin majalisar dokokin jihar Cross Rivers
'Yan majalisa sun tsige kakakin majalisar dokokin jihar Cross Rivers Hoto: @makesensepromot Asali: Twitter

Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa ƴan majalisar mutum 17 ne suka goyi bayan kuɗirin tsige kakakin daga muƙaminsa.

Honorabul Effiom Ekarika wanda ke wakiltar mazaɓar Calabar ta Kudu 1, shi ne ya gabatar da ƙudirin sannan Honorabul Omang Charles Omang, mai wakiltar mazabar Bekwarra ya mara masa baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Elvert Ayambem wanda yake wakiltar mazaɓar Ikom 2 an zaɓe shi a matsayin kakakin majalisar dokokin ne a ranar 10 ga watan Yunin 2023.

Wa'adin mulkinsa ya zo ƙarshe inda ko shekara ɗaya bai yi ba a kan kujerar saboda zarge-zargen da ake yi masa.

Ku dakaci ƙarin bayani.....

Asali: Legit.ng

People are also reading