Home Back

Sojoji Na Kan Bakarsu Na Tabbatar Da Tsaron Kasa – Shugaban Tsaro

leadership.ng 2024/7/6
Sojoji Na Kan Bakarsu Na Tabbatar Da Tsaron Kasa – Shugaban Tsaro

Babban hafsan hafsoshin tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa, ya ce kudurin rundunar sojin na tabbatar da tsaro abu ne mai muhimmanci gare su.

Janar Musa, ya bayyana hakan ne a cikin sakon gaisuwar Sallah ga sojojin da dukkan musulmi, inda ya bayyana cewa dakarun sojin Nijeriya na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsarin dimokuradiyya, kamar yadda a kwanan nan aka yi bikin cikar mulkin dimokradiyya shekaru 25 a Nijeriya.

Ya yi imanin cewa ‘yan Nijeriya, musamman jami’an soji, za su ci gaba da bin darussan sadaukarwa kamar yadda Annabi Ibrahim ya yi, yana mai ba da tabbacin ci gaba da jajircewar sojojin wajen maido da zaman lafiya da tsaro a Nijeriya tare da kare ta daga hare-haren cikin gida da na waje.

Janar Musa, ya yi amfani da wannan dama wajen nanata cewa rundunar sojojin, za ta ci gaba da yin amfani da hanyoyi daban-daban na ƙwarewa a kokarinta na tabbatar da tsaron kowane dan Nijeriya.

Daga ƙarshe Janar Musa ya yi kira ga ɗaukacin ‘yan Nijeriya da su rungumi zaman lafiya da haɗin kai da kaunar juna domin yaba wa kokarin sojojin kasar nan na faɗi tashi da suke ba dare ba rana wajen kare lafiya da tabbatar da haɗin kan ƙasa.

People are also reading