Home Back

'Yan Bindiga Sun Yi Yunƙurin Takaita Babban Limamin Musulmi a jihar Kaduna

legit.ng 6 days ago
  • Ƴan bindiga sun kai hari kauyen Gidan-Makera a ƙaramar hukumar Kagarko da ke jihar Kaduna, sun tafi da shanun babban limamin garin
  • Mazauna yankin sun bayyana cewa wasu ƴan banga sun yi nasarar kwato shanun bayan sun bi bayansu ranar Talata
  • Shu'aibu Ahmadu, wani mazaunin yankin ya ce limamin, Malam Ibrahim Zubairu ba ya gida lokacin da lamarin ya auku ranar Talata da yamma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - ‘Yan bindiga sun sace shanu 73 na babban limamin Gidan-Makeri, Malam Ibrahim Zubairu, a karamar hukumar Kagarko da ke jihar Kaduna.

Wani mazaunin kauyen Kuchimi da ke makwabtaka da Gidan-Makeri, Shuaibu Ahmadu ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata da misalin karfe 5:33 na yamma.

Taswirar jihar Kaduna
Yan bindiga sun yi yunkurin sace shanun babban limami a jihar Kaduna Asali: Original

Ya ce maharan ɗauke da miyagun bindigu kuma da adadi mai yawa sun kutsa kai yankin, kana suka yi yunƙurin sace shanun Malamin Addinin Musuluncin, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutumin ya ƙara da cewa daga zuwan ƴan bindigar suka wuce kai tsaye zuwa wurin da aka killace shanun a bayan garin, suka tattara su suka tafi.

Shu'aibu ya ce maharan sun riƙa harbe-harbe a iska domin tsorata mazauna garin kada su biyo bayansu a lokacin da suka kora shanun zuwa cikin jeji.

A cewarsa liman Malam Ibrahim ya yi tafiya zuwa Kagarko a lokacin da ƴan ta'addan suka kawo farmakin.

Yan banga sun kwato shanun liman

Bayan samun labarin abin da ya faru, ƴan banga daga kauyen Kachimi mai maƙwaftaka da Gdan-Makeri, suka bi sawun ƴan bindigar.

“Limamin yana Kagarko a lokacin amma da ikon Allah daga baya ’yan banga daga kauyen Kuchimi da ke makwabtaka suka kwato shanun daga hannun ƴan fashin dajin."

An tattaro cewa shanun sun yi gardama wajen tsallaka kogin Gurara, lamarin da ya tilasta wa ‘yan bindigar tserewa suka barsu a nan kafin isowar ‘yan banga.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Hassan Mansur, bai fitar da wata sanarwa a hukumance kan harin ba har kawo yanzu.

Matar aure ta kashe mijinta a Yobe

A wani rahoton ƴan sanda sun kama wata matar aure Zainab Isa bisa zargin daɓawa mijinta wuta har lahira a Abbari da ke cikin Damaturu a jihar Yobe

Mai magana da yawun ƴan sandan jihar DSP Dungus Abdulkareem ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da saɓani ya shiga tsakanin ma'auratan.

Asali: Legit.ng

People are also reading