Home Back

Yankin Masanaantun Sarrafa Goron Ruwa Da Sin Za Ta Gina A Angola Zai Inganta Baza Komar Tattalin Arziki

leadership.ng 4 days ago
Yankin Masanaantun Sarrafa Goron Ruwa Da Sin Za Ta Gina A Angola Zai Inganta Baza Komar Tattalin Arziki

An bayyana yankin masanaantun sarrafa goron ruwa da kasar Sin za ta gina a kasar Angola, zai samar da wani cikakken tsarin masanaanta da zai kunshi aikin harhada kayayyakin samar shi da narkarwa da ma sarrafa shi domin samar da kayayyaki, lamarin da zai bunkasa masanaantar da taimakawa kasar wajen baza komar tattalin arzikinta.

Yayin aza harsashin ginin yankin a Barra do Dande wanda ke lardin Bengo na arewa maso gabashin kasar, sakataren kula da harkokin masanaantu na kasar Carlos Rodriques, ya ce ana sa ran aikin ginin yankin masanaantun sarrafa goron ruwa na Huatong, zai gudana cikin matakai 5, wanda kuma zai lakume jarin dala biliyan 1.6.

Ya ce wannan muhimmin jari ya sake alamta gagarumin ci gaban da aka samu a ajandar hadin gwiwa ta Sin da Angola, yana mai cewa ana sa ran zai samar da guraben ayyukan yi 12,000.

Yayin bikin, jakadan Sin a Angola, Zhang Bin, ya ce irin wannan jari zai bunkasa kokarin Angola na baza komar tattalin arzikinta da bunkasa ayyukan masanaantu da samar da karin guraben ayyukan yi da kudin shiga da horar da masu basira. (Mai fassara: Faiza Mustapha)

People are also reading