Home Back

Paparoma ya jagoranci addu'o'in Paska na bana

dw.com 2024/5/9
Paparoma Francis a fadar Vatikan
Paparoma Francis a fadar Vatikan

Paparoma Francis ya jagoranci addu'o'in na Easter ne kuwa kwana guda bayan janye jiki da ya yi a kusan karshen addu'o'in Good Friday da aka yi a ranar Juma'a saboda dalilai na kare lafiyarsa.

Kodayake a jiya Asabar ma ya gabatar da wa'azi na mintuna 10 kuma ya yi wa wasu mutum takwas wankan-tsarki na Baptisma.

Cikin jawabin da ya gabatar a daren da ya gabata albarkacin bikin Easter da ake ciki, ya yi tir matuka a game da yake-yake da kuma kiyayya gami da kyamar juna a duniya.

Wasu dai na nuna damuwa game da yanayin lafiyar Paparoma Francis ganin yadda wasu daga cikin ayyukan ibadar lokacin na Easter suka wuce shi.

Fadar Vatikan ta ce yana fama ne da mura da kuma matsaloli da ke da nasaba da hanyoyin numfashi.

People are also reading