Home Back

Yunkurin sauya fasalin tafiyar da mulki a Najeriya

dw.com 2024/7/2
Muhammadu Buhari ne ya mika mulki ga Shugaba Bola Tinubu a ranar  ga watan Mayun
Muhammadu Buhari ne ya mika mulki ga Shugaba Bola Tinubu a ranar ga watan Mayun

An dade ana batun sauyin fasali, amma wannan shi ne karon farko da tarayyar Najeriya ke fuskantar sabon yunkurin sauya makomar mulki cikin kasar a banagren 'yan doka. Wasu jerin 'yan majalisa 35 da suke kiran kansu masu neman sauyi sun kai ga yunkurin sauya daukacin harkar mulki ta kasar. A cikin jerin bukatar da suka mika wa zauren majalisar wakilai, masu neman sauyin suka ce Najeriyar na da bukatar mai da wa‘adin mulki daya na shekaru guda shida. A yayin da za'a yi karba karbar mulkin a tsakanin shiyoyin kasar guda shida.

Shugaba da mataimaka daga sassan Najeriya?

Karkashin jagorancin Ikenga Ugochinyere masu neman sauyin na neman kaddamar da mataimaka guda biyu na shugaban kasa daga sassan kasar na Kudu da Aewa. Ya zuwa yanzu, Najeriya na cikin gwaji na shugaban kasa da ke da cikkaken iko, da ke zama gwaji na biyu tun bayan samun 'yancin kai. A baya, kasar ta gwada tsarin majalisar dokoki mai karfi, kafin juyin mulkin farko da ya dora kasar bisa tafarkin soja. Sai dai tun kafin a kai ga ko'ina, sabon tsarin ya fara daukar hankali cikin kasar.

Karin bayani:Kira kan kyautata mulki a Afirkai: 

Sabo Imam Gashuwa da ke zaman mataimakin shugaban jam'iyyar NNPP na kasa, reshen Arewa maso gabshin Najeriya ya ce sabon shirin na da launi da siga ta kabilanci cikin siyasa ta kasar. Ya ce: "Ni a wurine, ajenda ce ta kabila ta da yare, wadda masu wannan ajendar idan kaje garinsu da dogon kaya da hula sai ka biya haraji. Ni ya faru da ni. Na je garinsu sai da na biya Naira 2,000 a matsayin haraji. Wadannan mutane su ke fadin karba-karba. Mulki kawai a yi adalci ko wane kabila kake ko yare.‘‘

Karin bayani:Siyasar sauya sheka a Tarayyar Najeriya

Kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi sake gyara kundin kafin a iya kaiwa ga tabbatar da sauya tsarin tafi da harkar mulki ta kasar. A tunanin Hon. Magaji Da'u Aliyu da ke zaman tsohon dan majalisar wakilai,  abun da ke faruwa a zauren dokar na nuna alamun karyewa tafiyar da harkar doka a kasar. Ya ce: ‚‘‘ Abun mamaki shi ne, a cikin tashin hankalin da ake ciki yanzu, wani mai hankali ma ya kawo irin wannan batu. Lallai yanzu babu 'yan majalisa a Najeriya,‘‘

Tasirin sauya wa'adi zuwa shekaru shida

Sabobbin sauye-sauyen na dada nunin yatsa ya zuwa fadar shugaban kasa a cikin neman iko cikin kasar mai nisa. Sauyin tsarin mulkin na iya kai shugaban kasar zuwa wasu karin shekaru shida bayan hudun da ke a farkon fari. Faruk BB Faruk da ke sharhi kann batun siyasa ya ce rashin shugabanci na gari na zaman matsala a cikin Najeriya, ba wai salo na mulki na kasar ba. Ya ce: "A harkar siyasa, kowane tsari aka dauka, idan aka samu masu amana da jajircewa, suna kawo wa mutanensu ci-gaba. Ko da tsari aka yi na addinanci kamar Iran, ko sarauta kamar Dubai da Kuwait, ko kwaminisanci kamar Rasha da Kuba ba a shiga irin wannan yanayi ba.‘‘

A baya, shugaban kasar Goodluck Ebele Jonathan ya yi kokarin sake tsarin mulkin ba tare da kaiwa ga burge masu kokarin yin dokar ba. Ko bayan Chief Olusegun Obasanjo ma ya sha kafar kano bisa neman sauya wa'adin mulki ga kasar.

People are also reading