Ana Jita Jitar Tsige Sarkin Musulmi, Atiku Ya Ba da Shawara 1 Ta Kare Martabar Sarakuna
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya yi magana kan yadda gwamnoni ke taɓa rawunan sarakunan gargajiya a jihohinsu.
Atiku Abubakar ya ce abubuwan da ke faruwa a baya-bayan nan na tsige sarakuna a jihohi ya fara zama tamkar cin fuska ga sarautun gargajiya.
Dan takarar shugaban kasa karkashin PDP a 2023, ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku Abubakar ya ce duk da cewa masarautun gargajiya na karkashin kulawar kananan hukumomi, ya zama wajibi a rika kallonsu matsayin ginshikin da ya gina tsarin mulki.
Da wannan, Atiku ya ke ganin ya zama dole a kare masarautu daga gwamnatin jihohi musamman wadanda ke kokarin rusa tsarin gudanarwarsu.
Atiku ya ce:
"Idan har babu daidaito a tsarin gudanarwar sarakunanmu na gargajiya, hakan zai kawo cikas ga daidaita zaman lafiya da kwanciyar hankali a garuruwa."
A yayin da yake magana kan hanyoyin kare masarautu a Najeriya, tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce:
"A wannan gabar, ina mai yin kira da a sake fasalin kundin tsarin mulkin kasar nan domin sanya masarautu a cikin doka da kuma tsara gudanarwarsu.
"Wannan garambawul din zai kara taimakawa wajen dakile ta'addanci da kuma tabbatuwar tsaro a garuruwan ƙasar."
Atiku Abubakar ya ci gaba da cewa:
"Duk da cewa babu masarautu a cikin dokar kasarmu, sai dai abu ne a fili cewa sarakuna na taka rawa wajen ci gaban kasa da kuma wanzar da zaman lafiya.
"Masarautu na taimakawa wajen jagorantar jama'a, don haka dole ne mu kare martabarsu ba wai mu rusa su ba.
"Ina kira ga gwamnonin jihohi da su girmama sarakunan gargajiya. Jagorancin da sarakuna ke yi shi ke nuna ainihin al'adun mu tun na kaka da kakanni."
Wannan dai na zuwa ne awanni bayan da kungiyar MURIC ta yi zargin cewa gwamnatin jihar Sokoto na shirin tsige Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar.
Shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Litinin inda ya gargadi gwamnan jihar kan wargi da kujerar sarkin.
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sake aika sakon umarni ga Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero kan zamansa fadar Nasarawa.
Gwamnatin Kano ta umarci Aminu Bayero da ya gaggauta ficewa daga fadar Nasarawa domin ba ta damar gudanar da gyare-gyaren da ta shirya yi a karamar fadar sarkin.
Asali: Legit.ng