Home Back

Gwamna Radda Ya Kinkimo Wani Gagarumin Aiki da Zai Jagoranta a Arewa

legit.ng 2 days ago
  • Yayin da ake fama da yunwa a Najeriya, Gwamna Dikko Umaru Radda ya sha alwashin jagorantar yaki da rashin abinci mai gina jiki
  • Radda ya nuna damuwa kan yadda ake samun mutuwar yara kanana saboda rashin samun abinci mai gina jiki musamman a Arewa
  • Gwamnan ya bayyana haka ne yayin taron samar da mafita kan matsalar da aka gudanar a Abuja wanda wasu gwamnoni suka halarta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Katsina - Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina ya dauko wani babban aiki a Arewacin Najeriya.

Radda ya sha alwashin jagorantar gangamin yaki da rashin abinci mai gina jiki musamman a yankin Arewa.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin wani babban taro a birnin Abuja da ma'aikatar lafiya ta shirya, The Nation ta tattaro.

Dikko ya bayyana himmatuwarsa wurin ganin ya kawo walwala musamman ga mutanen jihar Katsina.

Ya nuna damuwa kan kididdigar da aka yi cewa akalla yara fiye da miliyan 10 ne ke fama da rashin abinci mai gina jiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Abin ya yi yawa kuma yana bukatar kulawa sosai, a katsina muna fuskantar rashin abinci mai gina jiki da yake damun al'umma."
"Wannna hakki ne da ya rataya a wuyanmu domin daukar matakan gaggawa da dabaru wurin magance matsalar."

- Dikko Umaru Radda

Taron ya samu halartar manyan mutane ta ko ina daga Najeriya da suka hada da gwamnonin jihohi.

Daga cikinsu akwai gwamnan Zamfara, Dauda Lawal da na Niger, Umar Bago da kuma mataimakin gwamnan jihar Kebbi.

Har ila yau, akwai ministan Lafiya, Dakta Ali Pate da kuma wakiliyar ma'aikatar noma, Sughra Mahmood.

Gwamnonin Arewa sun yi taro kan tsaro

Kun ji cewa Gwamnonin Arewa maso Yamma sun amince da wani tsari da wa'adi na kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi shiyyar.

Shugaban ƙungiyar gwamnonin a yankin, Dikko Umaru Radda ya bayyana hakan a karshen taron tsaro da zaman lafiya na shiyyar da ya gudana a Katsina.

Hakan ya bito bayan fama da matsalolin tsaron da ake fama da shi musamman a yankin Arewa maso Yamma.

Asali: Legit.ng

People are also reading