Home Back

Rashin isassun sojoji ya sa ake ci gaba da hare-haren ta’addanci a wasu sassan Najeriya – Ministan Tsaro

premiumtimesng.com 2024/4/28
Rashin isassun sojoji ya sa ake ci gaba da hare-haren ta’addanci a wasu sassan Najeriya – Ministan Tsaro

Ministan Harkokin Tsaro, Muhammad Badaru, ya bayyana cewa matsalar rashin wadatattun sojoji ne ya sa ‘yan ta’adda da mahara ‘yan bindiga ke ci gaba da kai hare-haren ta’addanci a wasu sassan Arewacin Najeriya.

Badaru wanda ya bayyana hakan a ranar Talata, ya ci gaba da cewa duk da waɗannan ƙalubale na rashin isassun sojojin da ake samu, zaratan na Najeriya su na ci gaba da daƙile gungu-gungun ‘yan ta’adda.

Badaru ya bada labarin yadda sojojin Najeriya a kwanakin nan suka samu nasarar kakkaɓe manyan gagarman ‘yan ta’adda har su bakwai.

“Maganar gaskiya babu isassun sojoji, shi ya sa abin da Ƴanbindiga ke yi, sai su samu yankunan da babu jami’an tsaro su riƙa kai hare-hare a can. Da sun kai hari kuma sai su gudu su tsere cikin daji.”

Batun rashin wadatattun sojoji da Badaru ya yi, ba shi ne karon farko da aka tayar da wannan gagarimar matsalar ba. Saboda ko Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya sun bayyana haka a lokacin da suka amsa gayyatar Majalisar Ƙasa.

Duk da tun asali aikin sojoji shi ne kare ƙasa daga hare-hare ko farmaki daga ƙasashen waje, matsalar tsaro a faɗin ƙasar nan ta sa an riƙa girke sojoji a kusan dukkan hanyoyin jihohi 36 na Najeriya da Abuja.

Gwamnatin Bola ta yi alƙawarin ɗaukar ɗimbin matasa aikin soja da sauran ɓangarorin hukumomin tsaro.

A ranar Talata, Minista Badaru ya yi tattaunawa da manema labarai, bayan ya yi jawabi ga Manyan Jami’an Sojoji na Kwas mai Lamba 46, a Babbar Kwalejin Horas da Manyan Sojoji ta Jaji, Kaduna.

Ministan wanda ya je ne a rangadin ziyara, ya yi jawabin yayin da ake gabatar da taron ƙara wa juna sani a kwalejin, kan salon daƙile mahara da ‘yan ta’adda.

Badaru ya ƙara da cewa, “Gwamnati ta maida himma sosai wajen ganin ta daƙile maharan ta’addanci, a wani tsarin inganta tsaro mai salon amfani da al’ummar yankuna.

“Mun ɗauko wannan gagarimin aiki, ɗaukar gaba-gaɗi, ta yadda za a samu nasarar kakkaɓe ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga baƙi ɗaya.”

Badaru ya bada tabbacin cewa za a kakkaɓe duk wasu gungun ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga.

Da ya ke rangandin duba wasu kayayyakin inganta tsaro a kwalejin, ya ce an tanadi kayan ne domin horas Da sojoji a samu zaratan musamman 2,400, waɗanda za su yi wa ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda kakkaɓar a-yi-ta-ta-ƙare.

Ya ce za a fara ne da horas da zarata 800 tukunna, waɗanda za su fara horaswa ɗin nan da watanni biyu.

 
People are also reading