Home Back

Shawarwarin Kasar Sin Sun Dace Da Bukatun Tabbatar Da Tsaron Duniya

leadership.ng 2024/6/29
Shawarwarin Kasar Sin Sun Dace Da Bukatun Tabbatar Da Tsaron Duniya

Yayin kammala taro kan tsaro na Shangri-La a Singapore a ranar Lahadi, tawagar kasar Sin ta ce kasar ta tabbatar da kiyaye zaman lafiya da tsaron kasa da kasa bisa ayyukanta masu amfani, ta yadda ta ba da gudummawa wajen samar da tsaron jama’a da kyautata zamantakewar kasa da kasa.

Tabbas salon kasar Sin game da batun tsaro da ma sauran batutuwa, ya fita daban da na sauran kasashen da suka ci gaba, domin ba ta kasance mai tayar da fitina ko takala ko kara rura wutar rikici ba, maimakon haka, ta kasance mai sulhu tsakanin bangarorin da ba sa jituwa, kuma mai kira da a hau teburin tattaunawa da tabbatar da adalci da kuma warware matsaloli tun daga tushe.

A ko da yaushe ta kan yi la’akari da moriyar da halaltattun hakkokin al’ummomin kasa da kasa, haka kuma ba ta sanya siyasa cikin al’ummarn da suka shafi rayuwar fararen hula. Yanayin zaman lafiya da al’ummar kasar ke morewa, ya isa tabbatar da cewa, hanyar kasar Sin na neman tsaro da wanzar da zaman lafiya, irinta ake bukata a daukacin duniya. Yayin taron na Shangri La, kasar Sin ta gabatar da wasu shawarwarin wanzar da tsaro a duniya. Daga cikinsu kuma, akwai kiyaye halaltacciyar moriyar tsaro ta dukkan kasashen duniya. Tabbas, kiyaye moriyar tsaro da cikakken ikon kasashe, abu ne mai muhimmancin gaske, domin rashin hakan shi ke ingiza rikici da tashe-tashen hankula. Duniya ta shaida yadda wasu kasashe ke yi katsalandan cikin harkokin gidan kasashen waje, lamarin da ya kasance babban abun dake haifar da rikice-rikicen da muke gani a yanzu. Wajibi ne kasashen duniya dake kiran kansu manya, su mayar da hankali ga harkokinsu na gida maimakon zuba kudi da bata lokaci wajen ingiza yake-yake a kasashen waje, domin hakan ba zai taba kawo zaman lafiyar da dan Adam ke muradi ba.

Haka kuma, Sin ta ce ya kamata a tabbatar da daidaito da adalci a tsakanin kasa da kasa. Dukkan kasashen duniya manya ko kanana, daya ne, babu wadda ta fi wata. A ganina, rashin girmamawar da wasu manyan kasashe ke yi wa wasu, yana taka muhimmiyar rawa wajen haifar da fitina ko nuna fin karfi ko kuma ta’azzarar rikice-rikice. Ana bukatar garambuwal a harkokin jagorantar duniya domin a rika jin muryoyin kasashe da dama ba wasu ’yan tsiraru kadai ba. Hakan, zai taka muhimmiyar rawa wajen samar da tsaro da zaman lafiya a duniya, da kuma kare kananan kasashe daga fin karfi da danniya.

Yanayin tsaro dake akwai a kasar Sin, daya ne daga cikin abubuwan da suke burge ni da kasar, kuma na yi imanin idan kasa da kasa za su yi amfani da shawarar kasar Sin, to dan Adam zai kasance cikin kwanciyar hankali, haka kuma za a samu jituwa tsakanin mabanbantan al’ummomi. (Fa’iza Mustapha)

People are also reading