Home Back

Karin Albashi: Tsohon Shugaban VON Ya Mika Bukata ga ’Yan Kwadago Kan Janye Yajin Aiki

legit.ng 2024/7/1
  • A yayin da kungiyar kwadago ta shiga yajin aiki a yau Litinin, mutane sun fara bayyana ra'ayoyinsu kan lamarin
  • Tsohon daraktan kafar yada labaran VON, Osita Okechukwu ya ba kungiyar hakuri kan janye yajin aikin da ta shiga
  • Osita Okechukwu ya fadi dalilai kan kiran janye yajin aikin tare da bayyana matakin da ya kamata NLC ta dauka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Al'ummar Najeriya sun fara bayyana ra'ayoyi kan yajin aikin da kungiyar kwadago ta fara a yau Litinin, 3 ga watan Yuni.

Tsohon dakatar kafar yada labaran VON, Cif Osita Okechukwu ya yi kira ga kungiyar ta janye yajin aikin cikin gaggawa.

Yajin aikin NLC
An roki kungiyar kwadago ta janye yajin aiki. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Nigeria Labour Congress HQ Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Osita Okechukwu ya ce janye yajin aikin shi ne mafita ga Najeriya a halin yanzu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yajin aiki zai jawo matsalar tattalin arziki

Osita Okechukwu ya ce yajin aikin da kungiyar kwadago ta shiga zai iya haifar da matsalar tattalin arziki ga Najeriya.

Ya kara da cewa idan kungiyar ba ta janye yajin aikin ba, za a iya samun tarin matsaloli da magance su zai dauki tsawon lokaci.

Yajin aiki: Okechukwu ya ba NLC hakuri

A cikin jawaban da Osita Okechukwu ya yi, ya ce kungiyar kwadago ta yi hakuri ta karbi tayin ₦60,000 da gwamnatin tarayya ta mata.

Ya ce a halin yanzu kasar ba ta da kudin da za ta iya biyan sama da ₦400,000 ga ma'aikata a fadin kasar.

Okechukwu ya kara da cewa ko da ₦30,000 da aka kara a matsayin mafi ƙarancin albashin, wasu jihohi da dama ba sa iya biya.

Saboda haka ya ce ya kamata kungiyar ta maida hankali kan tsarin mallakar gidaje ga ma'aikata da gwamnati ta kirkiro maimakon yajin aiki.

An biya 'yan fansho a Zamfara

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta biya yan fansho sama da 4,000 kudin da suka bi jihar bashi na tsawon shekaru 13.

Rahotanni sun tabbatar da cewa wadanda aka biya kudin sun hada da tsofaffin malaman makaranta da ma'aikatan ƙananan hukumomin jihar.

Asali: Legit.ng

People are also reading