Home Back

Kasashen Latin sun yi barazanar mayar da Ecuador saniyar ware akan Mexico

rfi.fr 2024/5/15
'Yan Sandan Ecuador a wajen ofishin jakadancin Mexico, bayan cafke tsohon shugaban kasar da ofishin ke bai wa mafaka.
'Yan Sandan Ecuador a wajen ofishin jakadancin Mexico, bayan cafke tsohon shugaban kasar da ofishin ke bai wa mafaka. REUTERS - Luis Cortes

Gwamnatocin kasashen yankin Latin ko na yankin Kudancin Amurka sun yi Allah wadai da Ecuador biyo bayan samamen da jami’an tsaron kasar suka kai kan ofishin jakadancin Mexico a birnin Quito, domin cafke tsohon mataimakin shugaban kasar ta Ecuador da ofishin ke bai wa mafaka.

Tuni dai kasashen biyu suka katse alakar diflomasiyar da ke tsakaninsu bayan aukuwar lamarin.

A ranar Asabar ne kuma kasashen Bolivia, Argentina, Brazil, Chile, Colombia, Cuba, Peru, Uruguay da kuma Venezuela suka yi amfani da kakkausan harshe wajen caccakar gwamnatin kasar ta Ecuador, sa’o’i bayan amfani da karfin da tayi wajen cafke tsohon mataimakin shugaban kasar Jorge Glas.

A ranar Juma’ar da ta gabata, jami’an tsaron Ecuador da suka yi tinjim cikin shigar yaki suka fasa ofishin jakadancin Mexico, tare da yin awon gaba da tsohon mataimakin shugaban kasar da karfin tsiya.

Bayanai sun ce tun cikin watan Disambar shekarar bara Jorge Glas ke boye a ofishin jakadancin na Mexico, bayan da gwamnatin Ecuador ta yi shelar nemansa ruwa a jallo, bisa tuhumarsa da laifukan cin hanci da rashawa.

People are also reading