Home Back

'Yan Ta’adda Sun Kashe Sojoji 21 a Harin Kwanton Ɓauna, Gwamnatin Nijar Ta Yi Martani

legit.ng 2024/7/4
  • Rahotanni sun bayyana cewa 'yan ta'adda da ake zargin 'yan kungiyar Al-Qaeda ne sun kashe sojojin Nijar 21 tare da jikkata wasu tara
  • An ce 'yan ta'addan sun yi wa sojojin kwanton ɓauna a Tassia Sun Badjo, yankin Yammacin Tillaberi, iyaka da Mali da Burkina Faso
  • Gwamnatin kasar Nijar ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku yayin da ta ce an kashe gwamman 'yan ta'addan a harin kasa da sama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ƙasar Nijar - Gwamnatin mulkin soja ta ƙasar Nijar ta ce wasu 'yan ta'adda sun kashe sojojin ƙasar 21 a wani harin kwantan ɓauna a ranar Talata.

Sanarwar da gwamnatin ta fitar a kafar talabijin ɗin kasar ta ce an yi wa sojojin kwanton ɓauna ne a Tassia Sun Badjo, yankin Yammacin Tillaberi.

Gwamnatin Nijar ta dauki mataki bayan 'yan ta'adda sun kashe sojojinta 21
'Yan ta'adda sun kashe sojojin Nijar 21 da jikkata wasu tara. Hoto: Reinnier Kaze/Stringer Asali: Getty Images

An kashe sojojin Nijar 21 da farar hula

Jaridar AP News ta ce sanarwar ta ranar Talata ba ta bayyana kungiyar ta'addanci da ta dauki nauyin kai harin ba, sai dai Nijar na fama da hare-hare daga kungiyoyin ta'addanci da dama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta kara da cewa an akwai farar hula guda daya da aka kashe a harin, yayin da sojoji tara suka samu raunuka.

Gwamnatin Nijar ta ce an kashe gwamman 'yan ta'addan a harin kasa da sama yayin da aka kai karin sojoji a yankin domin kakkabe maharan, kamar yadda jaridar France24 ta ruwaito.

Gwamnatin Nijar ta ayyana zaman makoki

An ruwaito cewa gwamnatin Nijar ta ayyana kwanaki uku na zaman makokin sojojin da aka kashe yayin da take neman hanyar magance faruwar hakan nan gaba.

Wannan harin dai an kai shi ne a iyakar Nijar, Burkina Faso da Mali, yankin da ƙungiyar ta'addanci ta Al-Qaida ta fi kai farmaki, in ji rahoton Zagazola Makama.

An ce hare-haren da 'yan bindiga ke kai wa yankunan saharar ya yi sanadin mutuwar dubunnan mutane da raba sama da miliyan biyu da muhallansu.

Sojojin Najeriya sun cafke 'yan bindiga

A wani labarin, mun ruwaito cewa sojojin Najeriya sun samu nasarar cafke 'yan bindiga da masu kai masu bindigogi a jihohin Kaduna da. Filato.

Wata sanarwa da rundunar sojojin ta OPSH ta fitar ta ce an kwato sama da bindigogi 30 da tarin alburusai yayin samamen da aka kai

Asali: Legit.ng

People are also reading