Yajin Aikin Ƴan Ƙwadago: Hukuma ta Bayyana Makomar Jarrabawar WAEC
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Ekiti- A lokacin da dalibai suka fara fargabar makomar jarrabawarsu ta kammala sakandare WAEC saboda yajin aikin kungiyoyin kwadago, hukumar shirya jarrabawar ta magantu.
Jami'a mai kula da hukumar reshen jihar Ekiti, T.A.Y Lawson yajin aikin gama-garin da za a fara ranar Litinin ba zai hana dalibai fitowa domin rubuta jarrabawar ba.
The Nation ta tattaro cewa hukumar ta bayyana cewa tana da masaniya kan shirin tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani da kungiyoyin kwadago za su fara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar shirya jarrabawar kammala makarantar sakandare ta WAEC ta bayyana dalilinta na cewa dalibai su fito su rubuta jarrabawarsu ranar Litinin duk da yajin aiki.
Jami;ar hukumar dake kula da jihar Ekit, T.A.Y Lawson ta bayyana cewa duk da sun tare da kungiyar kwadago 100%, amma bai kamata daliban su rasa jarrabawarsu ba, kamar yadda The Guardian ta wallafa.
Ta ce tunda ana rubuta jarrabawar WAEC a dukkanin kasashen dake Afrika ta yamma, bai kamata daliban Najeriya su rasa rubuta ta su ba.
Saboda haka ne T.A.Y Lawson ta umarci iyaye. malamai. masu duba jarrabawa, da dalibai su kwana cikin shirin rubuta jarrabawar kamar yadda aka tsara tun da fari.
A baya mun kawo muku rahoton cewa hukumar shirya jarrabawar WAEC a kasar Ghana ta rike sakamakon jarrabawar wasu dalibai daga makarantu 235 a kasar.
Jami''in hulda da jama'a na hukumar a Ghana, John Kapi ya ce an hanasu sakamakon jarrabawar ne saboda ana zarginsu da amfani da fasahar AI wajen amsa jarrabawar,.
Asali: Legit.ng